Daga Usman Nasidi
AKALLA mutane 7 ne suka rasa rayukansu, 7 sun jikkata, kuma saura ba a san inda suke ba a karamar hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi inda wani jirgin kwale-kwale dauke da mutane 150 ta kife cikin tekun Neja.
Shugaban hukumar kawo agaji na gaggawa wato NEMA na Jihar Sakkwato, Kebbi, da Zamfara, Alhaji Sulaiman Muhammad, ya tabbatar da faruwar wannan hadari a ranar Asabar.
Ya ce masunta da jami’an hukumar ruwan Najeriya na iyakar kokarinsu wajen nemo wadanda suka bace.
“Lokacin da muka samu labarin abin da ya faru, muka kira hukumar ruwa ta taimaka wajen ceto wadanda suka bace.
“Dukkan mutanen da ke cikin kwale-kwalen ne suka bace, yayin da ake bincike, an gano mutane 14; mutum 7 kuma sun mutu, sannan mutane 7 sun jikkata kuma suna asibitin Ngaski.”
NAIJ.com ta tattaro cewa hadarin ya faru ne yayin da kwale-kwalen ya ci karo da wata bishiya da ke cikin tekun, sai ya kife.