Rabo Haladu Daga Kadina
\’YAN yankin Sanata Sule Hunkuyi sun ce wakilin nasu ya gaza wakiltarsu
Wata kungiya a Jihar Kaduna na famar karbar sa-hannun jama\’ar yankin arewacin jihar domin yi wa Sanatan da ke wakiltar su kiranye bisa gazawarsa na yi masu wakilci a majalisar.
Sanata Sulaiman Hunkuyi dai na wakiltar arewacin Jihar ta Kaduna a majalisar dattawa
Kungiyar ta masu son yi wa Sanatan kiranye ta ce kawo yanzu ta samu nasarar tattara sa-hannun mutane fiye da dubu 10.
Ana dai zargin Sanata Hunkuyi da kasawa a majalisar, a inda masu son yi masa kiranyen suka ce bai taba kai kuduri ko daya a zauren majalisar ba.
Sai dai kuma wasu na bangaren Sanata Hunkuyi sun musanta zargin, a inda suke fadin cewa masu hamayya da Sanatan ne suke kitsa shirin yi masa kiranye.
Tuni dai da ma gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa dangane da batun, a inda ta ce tana tare da Sanata Hunkuyi kuma abin da kungiyar ke zargin Sanatan babu kanshin gaskiya a ciki.
Wasu dai na ganin idan batun yi wa Sanatan kiranye ya yi nasara to zai bude wani sabon babin masu zabe su rinka yi wa wakilan nasu kiranye idan ba sa yin abin da suke so ko yin abin da aka tura su yi na wakilcin jama\’arsu.