Matasa Dubu 10 Za Su Amfana Da Shirin N-Power A Adamawa- Gwamnatin Tarayya

0
790

 Muhammad Saleh, Daga Yola

GWAMNATIN tarayyar Najeriya ta tabbatar da matasa sama da dubu goma (10, 000) za su amfana da shirin tallafa wa matasa da gwamnatin tarayyar ta bullo dashi N-Power a Adamawa.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya bayyana haka a ziyarar aikin da ya kawo jihar,  domin bude aikin da wasu hanyoyin da gwamnatin jihar ta gina, ya ce lura da matsalolin da rikicin boko haram ya haifar a yankin yasa gwamnatin tarayya ta yi hubbasar ganin matasa sun amfana da shirin N-Power a yankin.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayyar za ta tabbatar ta sake gina garuruwan da \’yan kungiyar ta boko haram suka lalata, ya shawarci Nijeriya da su ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin tarayya, domin kuwa ta dauko hanyar samar da kyakkyawar canji ga kasar.

Tun da farko da yake gabatar da nashi jawabin gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla ya shaida wa mahalarta taron cewa gwamnatinsa ta samar da kyakkyawan sauyi ta bangaren gyara hanyoyi da ma gina wasu sababbi a jihar.

Da yake magana game da kudaden Paris Club kuwa Gwamna Bindow ya ce gwamnatinsa ta amshi kimanin kashi 70 cikin dari, ya ce kuma gwamnati ta kashe kashi 60 bisa dari na kudin wajen biyan albashi da fansho da garatuti.

A ziyarar ta mataimakin shugaban kasa a jihar, mai martala Lamido Adamawa Dokta Muhammad Barkindo Aliyu Mustafa ya karrama mataimakin shugaban kasar da mukamin Jagaban Adamawa.

An dai bayyana sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimainsa Yemi Osinbanjo a matsayin sunayen wasu manyan hanyoyi biyu a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here