Daga Usman Nasidi
SANATA Dino Melaye mai wakiltar Jihar Kogi ya bayyana cewa an yi kokarin ganin bayan rayuwarsa a jiya Asabar. Sai dai kuma har yanzu jami’an tsaro sun gagara cewa uffan game da lamarin.
Dino Melaye mai wakiltar Yammacin Kogi ya ce wasu ne suka kai masa hari a gidansa da ke Unguwar Ayetoro-Gbede da ke karamar Hukumar Ijumu a Jihar Kogi.
Sanata Melaye ya ce an dauki dogon lokaci ana luguden wuta a gidansa har aka dagargaza wasu motoci.
Sanatan ya ce an kama wasu daga cikin wadanda suka kai masa hari har su 7 cikin tsakar-dare.
Dino Melaye ya bayyana haka ne ta shafinsa na Twitter inda ya ce babu wanda zai iya ba shi tsoro a gwagwarmayarsa.
Hakazalika a wani labarin, Sanata mai wakiltar Kudancin Jihar Katsina watau Abu Ibrahim ya sha ruwan duwatsu da kasa yayin da ya kai ziyara mazabarsa ta garin Funtuwa.
A yanzu haka dai wasu Sanatoci da dama suna fuskanci irin wadannan barazanar na cin zarafin su da aka yi musamman a Arewa.