Sankarau Na Yaduwa A Yankunan Sakkwato

0
907

Rabo Haladu Daga Kaduna

MUTANE da dama sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar sankarau a Najeriya
A yayin da cutar sankarau wadda ta hallaka daruruwan rayuka ta fara lafawa a yankunan da ta fi kamari, bayanai na nuna cewa ana samun karuwar bullar cutar a wasu yankunan da babu ita da farko.
A Jihar Sakkwato, daya daga cikin jihohin da annobar ta shafa, mazauna wasu yankunan karkara na ci gaba da bayar da rahoton yadda cutar ta fara addabarsu.
Daya daga cikin garuruwan da cutar ta addabe su a yanzu shi ne Achida, da ke karamar hukumar Wurno inda ake fama da matsanancin zafi.
Mazauna yankin sun ce wannan cuta ta sankarau wadda babu ita a garin a da, na kara zama barazana a gare su, saboda kusan gidaje dai-dai ne babu mai cutar a ciki.
Mazauna yankin sun kara da cewa, a mako guda da ya gabata, a kowace rana sai mutum biyu zuwa uku sun mutu sakamakon kamuwa da cutar ta sankarau.
Bayan garin na Achida, akwai wasu yankunan yankin karamar hukumar tasu ma da cutar ta bulla har ma da rasa rayuka.
A karamar hukumar Gwadabawa , inda da cutar ba ta bulla ba, yanzu haka al\’ummar yankin sun ce cutar na addabarsu kwarai da gaske har ma an samu mace-mace a makon da ya gabata.
Alkaluman karshe da hukumomin Jihar ta Sakkwato suka bayar a kan adadin wadanda suka kamu da cutar a baya dai, ya kai mutum 600, inda 40 daga cikinsu suka rasu.
Jihar ta Sakkwato, na daga cikin jihohin da aka samu bullar cutar sankarau a bana, inda jihar Zamfara ta kasance jihar da annobar ta fi kamari tun da cutar ta barke, inda sama da mutum 200 suka mutu, kuma ake ba wa wasu da dama kulawa a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya.
Tuni dai ma\’aikatan kiwon lafiya a Najeriya suka fara rigakafin cutar ta sankarau a wani yunkurin na dakatar da ci gaba da yaduwar cutar.
Kuma nau\’in cutar sankarau da aka sani da \”meningitis type C\” wadda ba a saba samun aukuwar irinsa a Najeriya ba ne ya jawo barkewar annobar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here