\’Yadda Mahaifina Da Matarsa Suke Azabtar Da Ni\’, Ta Koka Ga Kungiyar Kwato Hakkin Dan Adam

0
809

Rabo Haladu, Daga Kaduna

ANA samun matsalolin kuntata wa yaran da iyayensu mata ba sa gida
Wata matashiyar yarinya \’yar shekara 20 ta ce mahaifinta bisa hadin gwiwar matarsa, yana azabtar da ita, a inda har yake yi mata barazanar korar ta daga gidansa.
Budurwar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai cewa mahaifin nata ne ya hana ta ci gaba da karatun jami\’a, a shekara ta biyu da karatun nata.
Ta kuma kara da cewa saboda ita marainiya ce ya sa matar uba ke zuga mahaifin nata domin ya dinga ci mata mutunci.
Matashiyar ta ce abin da ya fi bata mata rai shi ne, ba ta wa\’adin kwana biyu da aka yi domin ta fito da miji ko kuma a kore ta daga gidan na mahafinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here