Allah Ya Yi Wa Alhaji Amadu Chanchangi Rasuwa Yau Laraba 19-4-2017

0
1013

Zubairu Abdullahi, Daga Kaduna

DUBBAN daruruwan jama\’a ne suka halaarci jana\’izar fitaccen attajirin nan da aka fi sani da suna Alhaji Amadu Chanchangi wanda Allah SWT ya karbi rayuwarsa yau Laraba da safe bayan ya dade yana jinyar rashin lafiyar da take addabarsa a tsaye-tsaye, wadda ita ce ta zamo sila ga rasuwarsa.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi shi ne ya jagoranci sallar jana\’izar ta marigayin Alhaji Amadu Chanchangi.

Marigayi Alhaji Amadu Chanchangi ya yi suna matuka a hanyar taimakon addinin Allah, inda tuni bawan Allan ya shigar da dukiyarsa wajen tafiyar da ayyukan addinin Musulunci. Shugaba ne shi a rukunin kamfanonin sufurin jiragen sama na Chanchangi Airline.

Ya rasu ya bar matan aure da \’ya\’ya da dama. Dga cikin \’ya\’yansa akwai babban dansa da yake wakiltar al\’ummomin Kaduna ta kudu a majalisar dokokin tarayyar Najeriya, wato Honorabul Ahmad Rufa\’i Chanchangi.

Hukumar gudanarwar Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da kamfanin NNN na ta\’aziyya ga iyalan mamacin, Allah ya gafarta masa, ya sanya aljanna makomarsa ya sanya ayyukansa na alheri bisa mizaninsa,amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here