An Dakatar Da Sakataren Gwamnatin Tarayya Da Ambasada Oke

0
843

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SAKAMAKON saba wa aikin Gwamnatin Nijeriya ya haifar wa da wadansu manya-manyan jami\’an gwamnati gamuwa da fushin shugaba Muhammadu Buhari, inda ya dakatar da mutane biyu sakatararen gwamnati da shugaba leken asirin kasar.

Sakataren  gwamnatin Babachir David Lawan da Jakada  Ayo Muhammadu Oke shugban hukumar leken asiri duk an zarge su da batun almundahana.

Shi dai Babachir an dakatar da shi ne saboda zargin saba ka\’idar aikin gwamnati da aka bayar da wani aikin raya yankin arewacin arewa maso gabas na \’yan gidun hijira da \’yan boko haram suka lalata.

Shi kuwa Jakada Oke ya gamu da fushin ne sakamakon cewa da ya yi kudin da EFCC ta gano a Legas na hukumarsa ne.

Kamar yadda alkaluman suka nuna cewa kudin sun kai Naira Biliyan 13 lamarin da ya haifar da rudani.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina a cikin takardar da ya raba wa manema labarai ya ce shugaba Buhari ya bada umurnin gudanar da gagarumin bincike kan kudaden na Legas.

Binciken dai zai gano yadda hukumar ta NIA ta samu wadannan makudan kudade, kuma wana ne ya bada umurnin samar mata da kudin.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci kwamitin binciken mai mutane uku.

Sauran mutanen sun hada da ministan shiri\’ar kasar, Abubakar Malami, da mai bai wa shugaban kasar shawara ta fuskar tsaro Babagana Munguno.

Ana sa ran za su mika sakamon binciken cikin mako biyu.

Sanarwar ta ce manyan sakatarori a ofishoshin mutanen da aka dakatar su ne za su rike mukaman a lokacin da ake binciken.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here