Gwamnan Ebonyi Ya Haramta Shan Lemun Kwalba A Jiharsa

0
932

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

A Jihar Ebonyi Gwamnan jihar ya haramta shan lemun kwalba a wajen ko wace irin sabga a jihar saboda zargin da ake yawan yi na wasu daga cikin lemun kwalba a kasar nan na da hadarin gaske  David Umahi gwamnan jihar ne ya sanar da haka ranar Talata 18 ga wannan wata inda bayaninsa ya nuna, daga cikin lemunan kwalba da Umahi ya haramta shan su a jihar sun hada da  Coke, Sprite da kuma Fanta yayin da duk lokacin da aka zo yin wani sha\’ani na gwamnati a jihar.

Gwamnan wanda ya tara sarakuna gargajiya na jihar tare da sauran masu fada a ji a jihar shugabannin kungiyoyi matasa dana al’umma a ganawar da ya yi da su.

Wakilinmu na Kudanci ya kalato mana cewa, kwanan baya wata kotun tarayya da ke Legas ta yanke wani hukunci tsakanin kamfanin  Fijabi Adebo Holdings Limited, da Emmanuel Fijabi Adebo da suka yi karar kamfanin yin lemun kwalba na Nigerian Bottling Company Ltd da hukumar kula da ingancin abinci wato NAFDAC da suka yi zargin kamfanin na sarrafa lemun kwalba mara inganci suna sayar wa jama’a .kuma basu da isassun kayayyakin gina jiki na bitamin c duk da kamfanin ya fito  karyata zargin .

Waje daya kuma itama hukumar da ke kula da sarrafa kayan shaye-shaye  wato CPC a nata bangare kamar yadda wakilinmu ya ruwaito an ce lemun sha irin su Lucozade da ba kamfanin ke yi ba shi ma yana kunshe  da yawan kayan zaki a cikinsa.hukumar ta bukaci a yi bincike kan inganci da sahihancin kayan shaye-shayen.

Wata majiya da ke fadar gwamnatin ta sanar wa wannan jarida  cewa an ajiye lemunan kwalba irin su Sprite da Fanta da kuma Koka kola yana ganin su bayan ya zauna ya bayar da umarnin a kwashe su ya ce “ba za mu kara shan abin da zai halaka mu ba a jihar nan daga yau kada a kara yin amfani da duk wani lemun kwalba idan wata sabga ta tashi a jihar nan “inji Gwamnan

Daga nan ne fa aka ce Dogarai da ke gidan gwamnati da ma barori da ke raba lemunan suka fara kaye-kayen kwalben lemukan.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here