- Mustapha Imrana Abdullahi Daga Katsina
BAYANAN da ke fitowa daga Jihar Katsina na cewa an kama wata mata babbar ma\’aikaciyar jinya a asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina bisa zargin sayar da jariri kan kudi dubu dari biyu.
Sauran wadanda aka kama sun hada da wata uwar jaririn ta jini Ai\’sha Idris mai shekaru 18,da ke zaune a Unguwar Daki Tara Katsina Sai Hauwa Ibrahim , mai shekara 32 da ke Kofar Kaura da Misis Grace Ohuhu da Uba Kla a cikin Jihar Abiya.