Daga Usman Nasidi
BABBAN hafsan tsaro na kasa (CDS), Janar Abayomi Olanisakin, a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu ya ce, sojoji na musamman na samar da tabbataccen sakamako a harakar tsaro a yankin kudancin Kaduna.
Hafsan tsaron ya shaida wa manema labarai a Kaduna cewa `Operation Harbin Kunama ll, da aka kaddamar da mako daya da ta gabata ta kwace makamai daban-daban a yankin.
CDS ya ce sojojin na amfani da hanyoyin magance batun rashin tsaro a yankin ciki har da fashi da kuma barayin shanu.
A cewar shi, shugabannin gargajiya, addinai da kuma siyasa duk suna da hannu a cikin kokarin ganin cewa an tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Hafsan tsaron ya bayyana hakan ne a garin Kaduna yayin kaddamar da wata dakin taron mai mutane 1,000 a kwalejin kimiya na sojojin sama wato ‘Air Force Institute of Technology’.
Ya yaba wa babban hafsan sojan sama, Air Marshall Sadiq Abubakar domin hangen nesa da kuma abar koyi shugabanci.