Isah Ahmed, Jos
WANI dan kasuwa kuma shugaban matasa da ke zaune a garin Mista Ali a karamar hukumar Bassa da ke Jihar Filato, Alhaji Ubayo Danburam ya bayyana cewa a dukkan \’yan takarar shugaban karamar hukumar Bassa karkashin jam\’iyyar APC da suka fito, babu wanda ya cancanci ya zama shugaban karamar hukumar, kamar Farfesa Shem Binda. Alhaji Ubayo Danburam ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce babban dalilin da ya sa muke ganin cewa Farfesa Shem Binda ya fi kowa cancanta shi ne ya bada garurumar gudunmawa a wannan karamar hukuma musamman a fannin ilmi. Domin ya samar wa matasan wannan karamar hukuma makarantu a wurare daban daban na kasar nan. Kuma yanzu yana nan yana gina wata babbar makarantar gaba da sakandire a wannan karamar hukuma, don taimaka wa al\’ummar wannan karamar hukuma gabaki daya.
\’\’Bari yadda muka san halayen wannan dittijo wanda ya yi gwagwarmaya fannin ilmi a wurare da dama a Jihar Filato, babu shakka idan ya zama shugaban karamar hukuma Bassa, zai tafi da kowa da kowa batare da
nuna banbancin addini ko kabila ba. Don haka muke goyan bayansa a wannan takara\’\’.
Alhaji Ubayo Danburam ya yi bayanin cewa damu aka kafa jam\’iyyar APC a karamar hukumar Bassa, domin mun yi amfani da dukiyarmu da karfinmu wajen ganin wannan jam\’iyya ta kafu a wannan karamar hukumar.
Ya ce amma shugabar rikon da aka kawo mana wannan karamar hukuma Misis Sarah Bali, yanzu ta yi kusan shekaru biyu tana shugabancin wannan karamar hukuma amma bata yi mana komai ba.
Ya ce ta yi watsi da wadanda suka yi kokari wajen gina wannan jam\’iyya a karamar hukumar Bassa. Kuma babu abin da ta yi na kawo ci gaba a karamar hukumar Bassa.
Ya ce akwai wurare da dama da suke bukatar a taimaka masu wajen gyara masu makarantu da samar masu da wutar lantarki a wannan karamar hukuma, amma babu wani abu da wannan shugabar riko ta yi, kan irin
wadannan matsaloli.
Don haka ya yi kira ga al\’ummar hausa fulani da sauran al\’ummar wannan karamar hukuma su taru mu zabi Farfesa Shem Binda a zaben kananan hukumomin da za a gudanar a Jihar Filato, domin ya ceto wannan karamar hukuma daga mawuyacin halin da take ciki.