Daga Zubair Abdullahi Sada
TSOHON mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce Najeriya ko shakka babu Najeriya za ta ci gaba da samun matsaloli da suka shafi na rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki, muddin ba ta bi tsarin mulki tare da tabbatar da tana tafiyar da mulki bisa shimfidar da aka dora shi ba.
Atiku Abubakar ya yi wannan hange ne kuma ya furta hakan a lokacin da yake gabatar da wata kasida mai taken, \’\’Kalubalen Ci Gaba Da Na Zamantakewa, Kabilanci Da Ciyar Da Kasa\’\’ a wani taro da \’Daily Stream Newspaper ta shirya a dakin taro na Cibiyar Sojojin Sama da ke Kado a garin Abuja.
Ya ce, \’\’mulki da ake tafiyarwa a halin yanzu ya yi kama da mulkin a kasa a raba, ba na a yi aiki a zahiri ba ne, ba ya kuma haifar da komai sai koma baya a kasar nan\’\’.
Sai ya ce, kusan duk al\’amuran ci gaba da ya kamata a bi, ba su nan a kasa, sai dai yawan wahalhalu da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da dimbin rashin aikin yi ga jama\’a da dama, sannan ga hawa da sauka na kudaden kasashen ketare, ga karuwar jahilci na rashin karatu da dimbin yara da babu makaranta da sauransu.
\’\’Wajibi ne mu dawo cikin hayyacinmu mu hadu waje daya domin ciyar da kasar nan gaba. Mu cire son zuciya da son ranmu, mu agaza wa kasarmu ta gado\’\’. Inji shi.