WASU matasa ne su biyu dayan ana kiransa Ci-wake dayan kuma ana kiransa Adurguza , dukan su mashaya giya ne sun sha giya sun bugu sai dayan yana waka yana cewa Yesu na gabanmu yana bayanmu sai ya zo zai tsallaka titi sai Ci-wake ya ce Adurguza kar ka tsallaka-kar ka tsallaka ya kara cewa kar ka tsallaka –karka tsallaka .Sai Adurguza ya bi ya tsallaka titi sai mota ta buge shi sai Jonah ya ce wa wannan direba da ya kade Adurguza ya ce ka bi ka tafi abinka kurum sai direba ya tafi.
Sai ga ‘yan sanda suka zo suna dubawa sai Jonah ya zo ya fada wa ‘yan sanda yadda abin ya faru ya ce Adurguza ne ya taho yana waka yana cewa Yesu na gabanmu yana bayanmu sai mota ta bi ta durguje shi sai ya ce wa ‘yan sanda amma na bi na dauki lambar motar ‘yan sanda suka ce to mece ce lambar motar? Sai ya ce fi el [PL] amma sauran iska ta bi ta share sauran.
Daga Hashimu Hassan
Layin Bagobiri Kalaba
08096176141