Barayin Baturan Motoci Sun Addabi Unguwar Hausawa

0
972

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  Kalaba.

BARAYIN baturan motoci sun addabi Unguwar Hausawa da ke Layin Bagobiri Kalaba Jihar Kuros Riba manya da kananan motoci da suka zo dakon kaya daga sassa daban-daban na Nijeriya zuwa Kalaba musamman Layin Bagobiri nan wannan sace-sacen batur din mota ya fi kamari kana kuma  ma wasu daga cikin sasan babban birnin jihar su ma masu kananan motoci na shiga na kokawa da waccan matsala.

Bogobiri ,da aka fi sani da Unguwar Hausawa na daya daga cikin  babbar cibiyar kasuwanci a jihar musamman ga masu fataucin manja, ko goro zuwa sauran yankuna na kasar nan musammman arewacin kasa.Haka nan kuma ga masu hada-hadar musayar kudade na kasashen ketare hatta masu tafiya kasashen waje su Kamaru da Gabon da ma Afrika ta tsakiya wani lokaci sukan biyo ta wannan unguwa.

Kwatsam ranar  Alhamis da aka yi wani ruwan sama kamar da bakin  masaki wasu manyan motoci da suka yi lodin manja za su nufi jihohin Gombe da Kano sakamakon an gama masu lodi da dare kuma ga ruwan sama da ake yi ba hali su tafi cikin ruwa suka ajiye motocin su sai gari ya waye an dauke ruwa su tafi sai suka wayi gari an sace masu baturan motocin su guda hudu.

Kafin wanzuwar wannan matukar mutum zai bar motarsa ta kwana gefen titi to ya shirya sayen sabon batirin mota domin kafin gari ya waye barayin sun riga shi baturin motarsa.Wannan lamari da ya tsanata ya sanya direbobi masu dakon kaya suke hada-hada daga kudu zuwa arewa ko kuma daga can zuwa kudanci suka kirawo taron gaggawa domin daukar mataki na hana afkuwar haka.

Auwalu Yahudu ya shaida wa Gaskiya ta fi kwabo  bayan sun tashi taron cewa “babu yadda za a yi a ce cikin kwana bakwai an sace baturan mota shida a nan Bagobiri alhali muna biyan masu yi mana gadin motoci kuma mun yanke shawara duk lokacin da aka sake yi wa wani daga cikin mu satar baturin mota ba za mu yarda ba kara za mu kai masu gadin da kuma masu karbar kudin haraji da suke kin sallamar motocin mu a kan lokaci”inji Yahudu.

Wakilinmu a ganawar da suka yi da Hafiz Muhammad Inuwa ya tabbatar masa cewa boye bayanai na matsala da wasu jama’a kan yi wa rundunarsa ce ake gani kamar ba su daukar mataki amma da zarar an sanar wa ofisoshin ‘yan sanda mafi kusa za a dauki mataki “amma ya zuwa lokacin da muke hira da kai babu wani daga cikin jami’aina da ya samu labarin satar baturan motoci da ya yi kamari a Kalaba amma bakin kokari na bayar da tsaro da kuma kariya rundunata tana yi”.inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here