Daga Usman Nasidi
MATASA a garin Gololo da ke cikin Karamar Hukumar Gamawa ta Jihar Bauchi, sun fasa taron raba kayan tallafi da Dan Majalisar Tarayyar su ya shirya.
Dan Majalisa Honarabul Mohammed Garba Gololo ya shirya taron raba kayan ne a kauyen haihuwar sa, Gololo a ranar Lahadin da ta gabata.
Baya ga fasa taron, matasan sun kutsa kai cikin sabon gidan Dan Majalisar suka yi wa kayan gidan karkaf.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace talabijin, bidiyo, rikoda, firji, da duk wani abin amfanin da ke cikin gidan, hatta tagogin gidan sai da aka balle.
Ganau ba jiyau ba ta tabbatar wa majiyarmu cewa hatta motar da Mohammed Garba ke ciki sai da aka fasa gilashin ta yayin da ya yi niyyar ficewa daga wurin taron, inda matasa ‘yan baberiya suka nemi yi masa kofar-raggo suna cewa “Ba ma yi! Ba ma yi” , a lokaci guda kuma su na jifa.
Duk wani kokarin jin ta bakin sa ya ci tura, domin wayar sa a kashe ta ke. Sai dai daya daga cikin iyalansa ya tabbatar da cewa tabbas an fasa gidan an yi sata, amma aikin barayi ne, ba daga rudanin siyasa ba ne.
Wani dan garin mai suna Salisu, ya ce lokacin da abin ya faru yana cikin garin Gololo, amma ba a daki Honarabul ba, sai dai an fasa gilashin motarsa. Kuma a cewarsa, sharrin ‘yan adawa ne kawai.