GAWAR WANI MAMACI TA KAMA HANNUN DAN UWANSA DA KE MATA WANKA

0
1986
 Daga Usman Nasidi
JAMA\’A sun shiga zullumi tare da fargaba a ranar Litinin 1 ga watan Mayu a asibitin kwararru na garin Jos a lokacin da gawar wani mamaci da ake shirin biznewa ta yi wuf ta kamo hannun dan uwansa.
Wannan lamari mai cike da almara ya faru ne lokacin da gawar wani mutum mai suna Choji Zeng ta cafko hannun dan uwansa mai suna Gyang Zeng lokacin da \’yan uwansa suke yi masa wanka.
Ganin haka ya sa nan da nan sauran \’yan uwan da suke zagaye da gawar suka ranta ana kare, kowa na kiran kafa mai na ci ban baki ba! Amma ma’aikatan aisibitin sun yi karfin hali, inda suka shigo suka raba gawar da dan uwan nata.
Shi ma dan uwan mamacin, Gyang Zeng ya tabbatar ma maijiyar NAIJ.com faruwar lamarin, ya ce ya kammala wanke gawar dan uwan nasa, yana cikin sanya masa likkafani kenan, sai ya cafko masa hannu, ya ce nan fa ya sa ihu, yana neman agaji, har sai da ma’aikatan asibitin suka kwace shi.
Gyang ya ce “A lokacin da ya rike min hannu, sai na ce masa, haba Choji, so kake ni ma na bi ka, ko kuwa mene ne kake nufi ”?
Daya daga cikin ma’aikatan asibitin ya ce sun saba ganin irin haka na faruwa a asibitin. Amma wani makwabcin mamacin, Mista Benjamin ya shaida cewa, “ kafin rasuwan mamacin, sun samu rashin fahimta da kaninsa Zeng kan filayen gado, watakila shi ya sa ya kamo shi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here