AN KAMA WANI TSOHO DAN SHEKARA 60 DA SOYAYYEN SASSAN NAMAN MUTUM

0
965
Daga Usman Nasidi
RUNDUNAR \’yan sanda a Jihar Taraba ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wani dan shekara 60 mai suna Abubakar Abdulkadir da sassan jikin dan adam.
Mai magana da yawun rundunar \’yan sandan Mista David Misal shi ne ya bayyana hakan a ranar Juma\’a a ofishin \’yan sandan da ke a garin Jalingo.
A cewarsu, ana ma tunanin cewa soyayyen naman na mutun din da aka gan sa da shi na wani dan uwansa ne mai suna Ali Gimba wanda aka bayyana bacewar sa tun 27 ga watan Afrilu.
A wani labarin kuma, Rundunar \’yan sandan Najeriya shiyyar Jihar Oyo ta bayyana a ranar Juma\’ar da ta gabata cewa sun samu nasarar damke wani babban Fasto da kan mutum.
Sauran abubuwan da suka kama tare da Fasto din har da kan wata dabbar namun daji da kuma bindiga .
Haka ma dai rundunar \’yan sandan jihar ta kama wasu mutane 18 da suke zargi da laifin sata da fashi da makami sannan kuma da shiga kungiyar asiri.
Kwamishinan \’yan sandan jihar ya bayyana cewa shi dai Faston shi ne ya assasa cocin Cherubim da kuma cocin Seraphim, Idapomimo Zion, Alagbado, duka da ke a garin Legas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here