Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
AKALLA mutane 18 ne gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir Ahmad El-Rufa\’i, ta shelanta kamewa a game da batun rikicin da ya tashi tsakanin bangarori mazaunan Kabala ta yamma da kuma Unguwar Mu\’azu a cikin garin Kaduna arewacin Nijeriya.
Kamar yadda shugaban rundunar tabbatar da samun tsaro Kanar mai ritaya Yakubu Yusuf Soja ya bayyana wa manema labarai cewa mutane bangarorin biyu duk an same su dauke da makamai, don haka bisa tanajin doka za a kai su gaban kuliya domin yi wa kowa hukuncin da ya dace da shi.
\”Duk sun bayyana cewa sun yi hakan ne domin su kare kawunansu, amma babu inda aka ce mutum ya dauki doka a hannunsa\”. Inji Soja.
Sai dai a cikin wata sanarwar da mai Gwamna shawara kan harkokin yada labarai Mista Samuel Aruwan ya sanya wa hannu tayi bayanin cewa tuni aka tura wata tawaga da ta shafi Mai rikon sakataren Gwamnatin Jihar da Jami an tsaro na Jihar domin tattaunawa da bangarorin biyu.
Kuma a cewar sanarwar tuni an cimma matsayar cewa duk masu hannu a wannan lamari ya dace a zakulosu.
Ga masu bibiyar irin abubuwan da ke faruwa a dandalin sada zumunta na yanar Gizo sun ga irin yadda wasu marasa kishi da sanin yakamata suka rika yada karairayi har suna kiran jama a da su kiyayi hanyar shiga Kaduna daga Zariya.
Wanda hakan yasa jama a suka yi dafifi da ababen hawansu a garin marabar Jos da kuma Jaji saboda tsoron shiga garin na Kaduna.
An kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Kaduna da ta dauki mataki a kan jaridar naij ko naija dake yada karya a duk lokacin da wani abu ya faru a Kaduna saboda ko a kwanan baya ta yada cewa ana fada a Kaduna har an kashe wani Inyamuri.