MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
JAMI’IN hulda da jama,a na kungiyar muryar Tijjaniyya ta kasa Ustas Nasiru Zakiru Giwa Tazo ,Mina Jihar Neja ya fadi a Kalaba yayin zantawarsa da gaskiya Ta Fi Kwabo, cewa kungiyar muryar Tijjaniyya a duk inda take a Nijeriya kungiya ce wadda da ke kara hada kan al’ummar musulmi da kuma dangantaka tsakanin su har ma da wadanda suke ba musulmi ba .
Ustas Giwa Tazo ya ci gaba da cewa “wannna kungiya bayan hada kan ‘yan Tijjaniya da take ko ina a Nijeriya da sauran kasashen Nahiyar Afrika domin mu rika yin magana da murya daya”. Kuma haka da wayar da kan ‘yan kungiyar kan siyasa da sauran ma’amaloli na zamantakewa da na duniya, wannan na daya daga cikin dalilan da suka sanya aka kafa kungiyar a shekara ta 2012, kungiyar yanzu haka tanada rassa guda 29 a fadin kasar nan kowace kusurwa’’.
Ustas Zakiru Giwa ya ci gaba da cewa “haka nan kuma muna kokarin wayar da kan mutanenmu na su fahimci illar da ke tattare da yin watsi da yankin arewa a kowane lokaci aka yi zabe na siyasa aka kafa gwamnati.Da yake karin haske game da aikace-aikacen kungiyar kakakin muryar Tijjaniyya ta kasa ya kara da cewa “kowane lokaci idan azumin watan Ramadan ya kama wannan kunigya tana tallafa wa marasa galihu da gajiyayyu da abin da ya shafi kayan abinci da tufafi , ba mu ma tsaya a nan ba kadai har ma da marayu da kuma matan da mazajensu suka mutu suka bar su da marayu,domin rayuwar su su ma ta inganta “.
Karshe ya bukaci al’ummar musulmi su ci gaba da hada kansu kana kuma su zauna lafiya da junansu da ma wadanda suke kishiyar addininsu.ya yi wa kasa addu’a tare da fatar alheri gareta.