Gwamna Lalong Zai Mayar Da Kasuwar Shanu Ta Bukur Babbar Kasuwar Shanu A Nijeriya-Bala Muhammad

    0
    932
    Isah Ahmed, Jos
    ALHAJI Bala Muhammad shi ne  shugaban hadaddiyar kasuwar shanun nan, ta garin Bukur da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana tarihin kasuwar da irin gwagwarmayar da suka yi da tsohuwar gwamnatin Jonah Jang da ta gabata da kuma alkawarin da Gwamna Lalong ya yi na mayar da wannan kasuwa irin ta zamani. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
    GTK; Mene ne takaitatcen tarihin wannan kasuwa?
    Bala Muhammad; Ita dai wannan kasuwa asalinta matattarar shanu ce wadda Turawa suka kafa ta ne tun a shekarar 1944. Kuma Turawa sun kafa wannan waje ne da manufar  duk shanun da aka fito da su daga yankin
    arewa wadanda ake son a tafi da su zuwa yankin kudancin qasar nan. Nan ake tara su huta  a duba lafiyarsu kafin a tafi da su zuwa kudancin kasar nan.
    A nan a haka har masu sayen shanu da mahauta daga nan cikin garin Bukur da garin Jos, suka fara zuwa suna sayen shanun. Daga nan har wannan kasuwa ta zama wata babbar kasuwar shanu a wannan gari na Bukur.
    Tun daga wannan lokaci kasuwar ta ci gaba da bunqasa ta hanyar tara shanu. Domin an rika  kawo shanu daga  yankunan  wannan jiha ta Filato da yankin jihar Bauci  yankin Saminaka da Kafanchan da ke jihar Kaduna.  Yanzu wannan kasuwa ta bunkasa domin ana kawo shanu daga dukkan jihohin da suke makwabtaka da wannan jiha.
    GTK; Wanne irin kalubale ne kuka taba fuskanta a wannan kasuwa tun daga lokacin da aka kafa ta zuwa yanzu?
    Bala Muhammad;  Tun daga lokacin da aka buxe wannan kasuwa  ba mu taba samun wata barazana ba, sai  a lokacin  gwamnatin da ta gabata ta tsohon gwamnan jihar nan Jonah Jang. A lokacin da aka sami rikicin  farko a jihar nan na shekara ta 2001, wato zamanin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Joshua Dariye har aka gama
    wannan rikici, babu abin da ya faru a wannan kasuwa.
    Amma  a lokacin da aka sami rikici a gwamnatin  Jonah Jang a shekarar 2010, an zo an qona kasuwar nan gabaki daya. Aka kashe mana mutane aka kona mana motoci da shaguna kuma aka  kore mana shanu sama da guda 150. Wannan shi ne babban kalubalen da muka taba samu a wannan kasuwa.
    Sannan kuma bayan an yi mana wannan barna  babu abin da gwamnatin jihar nan ta yi na tallafa mana. Babban tallafin da karamar hukumar Jos ta kudu ta yi mana a lokacin shi ne ta ce mu tattara yanamu-yanamu mu tashi mu bar wannan kasuwa. Duk da haka muka ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinmu. Daga nan  sai gwamnatin jiha a lokacin  ta ce ta cire wannan kasuwa daga wajen da take ta mayar da ita bayan gari.
    Gwamnatin ta ce za ta yi filin wasa ne a wajen. Aka mayar da wannan kasuwa zuwa bayan gari, wajen da  babu wanda zai iya zuwa  saboda rashin zaman lafiya. Muna cikin wannan hali har Allah ya kawo canjin gwamnati.
    GTK; To, yanzu wanne hali ake ciki a wannan kasuwa?
    Alhaji Bala Muhammad; Halin da ake ciki a wannan kasuwa kamar yadda na ce tun daga lokacin da Allah ya kawo mana canjin gwamnati mun gode Allah. Domin zuwan wannan gwamnati sai muka sami sauqin al\’amura  tun daga karamar hukumar Jos ta kudu har ya zuwa  gwamnatin jiha sun karbe mu hannu bibbiyu. Domin daga zuwan wannan sabuwar gwamnati shugaban riko na wannan karamar hukuma ya ce mu je mu ci gaba da gudanar da harkokinmu a wannan kasuwa.
    Sannan kuma gwamnatin jiha karkashin Gwamna Lalong gaskiya babu abin da za mu ce sai godiya. Tun daga ma\’aikatar gona ta jiha wadda wannan kasuwa take karkashinta gaskiya mun sami taimako wajen tausaya mana ta hanyar kudurin inganta wannan kasuwa. Kwamishiniyar aikin gona ta jihar nan  ta kuduri aniyar inganta wannan kasuwa.
    Gwamna Lalong ya ce  a gina wannan kasuwa ta zama kasuwar  zamani  a yi shaguna  ayi banki da ofishin \’yan sanda da asibitin dabbobi a wannan kasuwa.  Don haka tuni har an kawo kamfanin da zai yi  aikin gina wannan kasuwa.
    Domin Gwamna Simon Lalong ya nuna cewa  yana son ya mayar da wannan kasuwar shanu ta Bukur babbar kasuwar shanu a Nijeriya.
    Kuma yanzu harkokin kasuwanci suna ci gaba a wannan kasuwa musamman saboda zaman lafiyar da aka samu a wannan jiha.  Yanzu baki masu kawo shanu suna zuwa daga wurare daban-daban kamar daga  makwabtan wannan jiha.  Haka kuma baki masu sayen shanu daga cikin wannan jiha har ya zuwa jihohin da suke makwabtaka da wannan jiha da kudancin kasar nan duk suna zuwa sayen shanu a wannan kasuwa.
    GTK; Mene ne kake ganin ya kwao tsadar dabbobi kasar nan?
    Bala Muhammad; Dalilan da suka kawo tashin dabbobi a kasar nan suna da yawa dalili na farko shi ne tashin  farashin  kayayyaki  a kasar nan. Tun da komai ya yi tsada dole ne ita ma saniya tayi tsada. Haka  kuma an sami wannan  tashin farashin  ne sakamakon nakasa kasar nan ne da gwamnatin da ta gabata ta yi.
    Bayan haka sakamkon rikicin boko haram an rasa dubban shanu a arewacin kasar nan kamar a jihohin Barno da Yobe. A lokacin wannan rikici an yanke samun shanu daga wadannan wurare.
    Sannan kuma ga karuwar  yawan da aka samu a kasar nan. Wadannan su ne dalilan da suka kawo tsadar shanu a kasar nan.
    GTK; Wanne irin gudunmawa ne kake ganin harkokin kasuwancin shanu yake bayarwa a kasar nan wajen bunkasa tattalin arziki?
    Bala Muhammad; Idan gwamnatin Nijeriya ta inganta abin da ya shafi saniya. Tun daga kiwon ta zuwa ga yanka. Babu abin da zai kawo bunqasa tattalin arzikin kasar nan kamar saniya. Domin saniya tana bayar da
    nama tana bayar da taki tana bayar da nono da noma. Domin a kasar nan motar noma ta gagari talaka don haka talakawa da dama sun koma yin noma da shanu a kasar nan.
    GTK; To, a karshe wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga masu harkokin kasuwancin sayar da shanu na kasar nan?
    Bala Muhammad; Sakon da nake da shi zuwa ga masu harkar kasuwancin dabbobi shi ne mu inganta wannan harkokin kasuwanci namu. Mu tsare mutuncin wannan kasuwanci namu. Domin akwai masu bata mana al\’amuran kasuwancin dabbobi a kasar nan.
    Akwai masu sato shanun mutane su kawo kasuwa kuma a batar da wadannan shanu da aka sato. Don haka ina kira ga \’yan kasuwarmu na shanu na kasar nan gabaki daya mu taimaka wa Fulani makiyaya wajen magance
    matsalar sace-sacen shanu a kasar nan. Domin idan babu saniya babu kasuwancinmu.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here