Majalisar Wakilai Tana Goyan Bayan Buhari Dari Bisa Dari- Alhassan Ado

2
875
Isah, Ahmed, Jos
BABBAN mai tsawatarwa na majalisar wakilai ta tarayya Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa majalisar wakilai ta tarayya tana goyan bayan kudurorin da shugaban kasa Muhammad Buhari, ya sanya a gaba na ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ta shiga dari bisa dari.
Alhaji Alhassan Ado Doguwa  ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron yaye daliban makarantar kiwon lafiya da koyar da ilmin kwanfuta [SYHCO] da ke garin Saminaka da ke jihar Kaduna da aka gudanar a garin Saminaka.
Ya ce duk wani mai kishin Nijeriya babu abin da zai yi,  sai dai ya yiwa Allah godiya da ya kawo shugaban kasa Muhammad Buhari, musamman a wannan lokaci da kusan komai ya tabarbare a Nijeriya.
Ya ce a iyakar fahimtata zuwan shugaban kasa Muhammad Buhari kan shugabancin kasar nan, kamar wani ceto ne da Allah ya kawo wa Nijeriya daga rugujewa.
\’\’Ina son na tabbatar cewa  a matsayinmu na abokan aikinsa  majalisar wakilai ta tarayya tana goyan bayansa dari bisa dari. Don cimma burinsa na kyautata hada-hadar kudaden gwamnati da inganta tattalin arzikin kasar nan\’\’.
Alhaji Alhassan Ado ya yi bayanin cewa  a halin da ake ciki majalisar wakilai ta tarayya ta  kusa kammala dukkan ayyukan da ya kamata ta yi kan kasafin kudi na shekara ta 2017.
Ya ce  kashi 85 bisa 100 na abubuwan da shugaban kasa Buhari ya gabatar wa majalisar kan kasafin kudi na shekara ta 2017  sun ba shi dama ya aiwatar da su. Domin  hakki ne na al\’ummar Nijeriya a kan majalisar ta bai wa shugaban kasa  kyakyawan hadin kai kan kudurorinsa.
Ya  yaba wa hukumar gudanarwar wannan makaranta kan kokarin da suke yi wajen taimaka wa al\’umma, ta hanyar tafiyar da wannan makaranta. Ya ce babu shakka wannan wani babban abin koyi ne ga sauran al\’ummar kasa gabaki daya.
Daga nan ya bai wa makarantar gudunmawar kudi Naira Dubu 500  da na\’urar kwanfuta da keken dinki ga dalibar da ta fi kwazo a cikin daliban da aka yaye.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban makarantar Malam Yakubu Ahmad Abubakar ya yi bayanin cewa  sun bude wannan makaranta ne don ganin sun ilmintar da al\’ummar wannan yanki kan ilmin kiwon lafiya da ilmin
kwanfuta. Domin yanzu duniya tana tafiya da wannan tsari ne.
Ya ce a wannan yaye dalibai karo na biyu  sun yaye dalibai guda 56 wadanda suka karantar da su kula da jinya da kuma dalibai guda 12 da suka karantar da su ilmin kwanfuta.
Ya ce a  yanzu  suna da dalibai guda 105  a wannan makaranta wadanda suka fito daga  yankin Doguwa da ke Jihar Kano da yankin Toro da ke Jihar Bauci  da kuma yankin Bassa da ke Jihar Filato.
Ya ce babban abin da suka  sanya  a gaba shi ne  bude asibiti a wannan makaranta, don taimaka wa al\’umma.

2 COMMENTS

  1. koh kugoya masa baya koh karku Goya masa baya mu talakawa muna tare dashi in allah kuma yabahi saiki

  2. koh kugoya masa baya koh karku Goya masa baya mu talakawa muna tare dashi in allah kuma yabahi saiki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here