Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna
WADANSU Fulani makiyaya da ke zaune a cikin Jihar Kaduna karkashin kungiyar ci gaban Fulani ta kasa wato (Fulani Development Association Of Nigeria) sun koka dangane da ci gaban satar masu shanu.
\’Ya\’yan kungiyar sun koka a gaban manema labarai a Kaduna inda wasunsu suka koka cewa cikin watanni uku hakika barayin Shanu sun zalince su matuka.
Sun shaida wa manema labarai cewa duk da dimbin kudin da Gwamnatin jihar karkashin El-Rufa\’i, ke kururuwar kashewa har yanzu satar shanun ma said karuwa kawai take yi a duk rana.
Sun tabbatar wa da manema labarai cewa a kasa da Watannu uku an Sace masu Shanu Dubu 11,571kuma barayin shanun sun aikata hakanne a cikin kananan hukumomi hudu kawai.
Kananan hukumomi su ne Chikun, Kjuru, Kachiya da Igabi. Kuma kamar yadda suka ce barayin suna tafiya ne da miyagun makamai kamar muguwar bindigar Mai Harbin makaman barkatai da irinsu bindigar AK-47 Wanda hakan yasa abune Mai wahala ga duk wani Bafulatani ya fuskancesu a yanayin da suke.