An Sami Wani Matashi Dan Baiwa A Fagen Kimiyya Da Fasaha A Katsina

0
1517

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A kokarinsa na ganin ya tallafa wa kasa da irin fasahar da Allah ya ba shi, matashi Abdurrahman Abubakar daga karamar hukumar Faskari a Unguwar Sarki Sheme Jihar Katsina ya kirkiro jirgin sama, tarakata da jirgin kasa, mashin boza,tankin mai da baro har da bene na sillen kara duk domin ciyar da Nijeriya gaba.
Wannan matashi akalla dan shekaru 17 an zo da shi garin Kaduna ne domin ya samu a bayyana wa duniya ko Allah zai kawo mai taimaka masa a samu ciyar da fasaharshi gaba.
Abdurrahman Abubakar ya bayyana cewa shi bai yi makarantar boko ba amma ya yi karatun Allo kuma saboda aikin gona a kauye ba a sa shi a makarantar boko ba, amma yana da basira kwarai.
\”Ni da kaina na kirkiri duk wadannan abubuwa da na lissafa maku duk da wasu a garinmu suna cewa ba zan iya ba amma Allah ya taimake mu muka kammala komai cikin nasara har kai da a Kaduna aka Kai ni filin jirgin sama domin in ga yadda jirgin sama yake ko ni ma in kAara basira\”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here