Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna
WANI babban jami\’in kiwon lafiya a Jihar Kebbi mai suna Lurwanu Gulan, ya tabbatar wa da manema labarai cewa akalla mutane hamsin ne suka rasa rayukansu a sakamakon hadarin motar da ya faru a kan hanyar Tsamiya zuwa Bagudo.
Jami\’in Lurwanu ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC mai yada shirye shiryenta a harshen Hausa cewa wata babbar motar Tirela ce mai daukar shanu daga kasuwar kauye ta dauki mutane tare da dakon shanun akalla da mutane dari a saman kayan.
Kamar yadda Lurwanu ya bayyana cewa a bisa al\’adar mutanen kauye da ke neman arha idan motar daukar shanu ta zo duk ranar kasuwa sai su kuma su hau saman kayan shanun da aka dauka saboda ana daukarsu kyauta ne.
\”A lokacin da motar tazo wajen wadansu ramuka uku sai direban ya yi kokarin ya kaucewa ramukan amma nan take Sai bodin motar ya cire ya kuma yi watsi da dukkan mutanen da ke sama nan take akalla mutane hamsin suka mutu bayan an kwashi wadansu kuma an kai asibiti, nan ma sai suka ci gaba da mutuwa bayan wadanda suka ji raunuka\”.Inji Lurwanu.
Ya ci gaba da bayanin cewa motar a kodayaushe tana dauke kayan shanu ne daga wadansu kasuwannin kan iyakoki a Jamhuriyar Nijar da Benin zuwa Legas Don haka Sai masu son arha su rika hawan saman shanu wasu a sauke su a Bagudo wasu Tsamiya da dai sauran garuruwa, daga nan sai motar ta wuce Legas kai tsaye.
Da yake fayyace yadda lamarin ya faru ya ce\”bayan bodin motar ya cire sai ya danne wasu tare da sossoke wasu da kahonnin shanun suka yi, inda nan take muka lissafa wadanda suka mutu mutane sama da hamsin an kuma samu karin wadanda suka mutu a asibiti da adadin ya kai hamsin da shida amma babu alkalumma a hukumance, sai dai mu da muka gani da idanunmu. Amma a gaskiya ban taba ganin tashin hankali na mutuwa irin wannan ba saboda na ga irin yadda shanu ke soke mutane da kaho har mutum ya mutu nan take ko kuma bodin babbar mota Tirela ya latse mutum ya mutu ban da kayan da suka rika danne jama\’a\”. Inji shi.