‘Yan Wasan Kwandon Kuros Riba Sun Tafi Inugu Wasan Sakandare

    0
    734

    MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

    AN bukaci tawagar ‘yan wasan kwallon kwando na shiyya da kamfanin Milo ya sanya da za a yi a Enugu rukunin ‘yan makarantar sakandare da su zage damtse su kankaro jihar wajen lashe mata zinare da gwala-gwale a gasar shugaban hukumar wasanni ta jihar Honarabul Orok Duke ne ya bukaci hakan yayin da ya ke yi wa ‘yan tawagar jawabin ban kwana.Ya ci gaba da cewa “ku zage damtse fa ku ciwo wa jihar nan zinare”.inji shi.

    Ya kara da cewa su zama jakadun Jihar Kuros Riba nagari yayin gudanar da wasan da zaman da za su yi a lokacin a can garin Enugu, ya ci gaba da cewa za su sanya ido a kan ‘yan wasan da kuma duk wani kokari da za su yi tun daga ranar da suka bar Kalaba zuwa Enugu har su dawo.nasara daga Allah take ka da ku ce sai kun kashe kanku wajen nemo wa jihar ku nasara ku dage ku yi bakin kokarin ku .

    Daga nan ya koka game da kasa a gwiwa da masu daukar nauyin gasar suka yi a shekarun baya idan aka kwatanta da ‘yan shekarun nan wajen namijin kokarin da suke yi idan lokacin gasar ya zo.

    A karshe ya bai wa iyayen ‘ya’yan da suka wakilci jihar tabbacin kare mutunci da lafiyar ‘ya’yan nasu har su je su dawo.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here