MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
AN nada sababbin shugabannin hukumar alhazai ta Jihar Kuros Riba wadanda aka nada sun hada da Alhaji Tanimu Hassan matsayin shugaban hukumar yayin da Alhaji Abdullahi Orok a zaman sakatare,kana kuma Alhaji Sani Aliyu Abdullahi da Ismahi Osho,da Alhaji Audu Bello Memba . Cikin wata sanarwar da aka aike wa manema labarai a Kalaba wadda ke dauke da sanya hannun kwamishinar yada labarai da wayar da kan jama’a ta jihar, Rose Mary Effiom Archibong, nadin nasu ya fara aiki nan take .
Bayan kammala kaddamar da shugaban da membobinsa Gaskiya Ta Fi Kwabo ta kebe Alhaji Tanimu Hassan shugaban hukumar Alhazai na hudu domin jin ta bakinsa game da wannan matsayi da Allah ya ba shi sai ya ce “Gaskiya ba karamin farin ciki na ji ba game da wannan mukami da Gwamna ya bani ,na dade ina neman wannan mukami tun lokacin tsohon Gwamna Sanata Liyel Imoke,to amma tun da Allah bai ba ni ba a lokacin ban damu ba, yau da Allah ya ce rabona ne to ga shi cikin ruwan sanyi aka kira ni aka ba ni”inji shi.
Hukumar Alhazai ta Jihar Kuros Riba ta sha kalubale na matsaloli ta mu’amala tsakanin jama’a da hukumarsa ko yaya sabon shugaban hukumar alhazan Kuros Riba zai tunkari wadancan matsaloli ya kuma magance su sai ya ce “Da taimakon Allah da na al’ummar jiha zan yi bakin kokarina to amma ba fariya ba yadda jama’a dari-bisa dari suka nuna min goyon bayan su da farin cikin su na wannan sabon matsayi da Allah ya dora min fatana shi ne Allah ya sanya ni a hanya tagari”.Ya roki jama’a da idan ya yi wani kuskure ba gefe za su rika komawa ba suna yin gunaguni ba su rika zuwa suna nuna masa domin ya gyara “Kuma ina rokon jama’a duk kuskuren da na yi ko zan bar kan hanyar ofishi na a bude yake ya kawo min shawara yadda za mu tafiyar da aiki tun da musulmi muke yi wa aiki”.