Har Yanzu Ba A Cimma Matsaya Ba A Rikicin Masu Kayan Gwari Na Ikom

0
886

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

AN shafe sama da sa’o’i biyar ana ta yamutsa gashin baki tsakanin Okimaka basaraken Ikom da kungiyar dillalan kayan gwari da kuma wadanda suka tibure su ba za su shiga kungiyar ba a fadar basaraken zaman da aka yi na ranar Asabar shida ga watan da muke ciki amma ba a kai ga cimma wata matsaya kwakkwara ba tsakanin ‘yan kasuwar da fadar basaraken ba.

Abin da ya jawo wannan ka-ce-na-ce tsakanin su  shi ne wasu mutum biyu Ibrahim da kuma ‘ya’yan limamin Ikom Malam Isyaku Muhammad Yahaya da kuma Daiyabu da hada baki da ‘yan asalin garin Ikom na zaluntar masu saye da sayar da kayan gwari a kasuwar ta kowace shekara da kan ci tsawon kwanaki 90.Da su ne suka kulla makirci a kan lallai ai Hausawa suna samun kudi a wannan harka dole su shigo kungiyar su mai hade da ‘yan asalin garin da kuma tsirarun ‘yan arewar da dukkanin su ba ma   sana’ar kayan gwari suke yi ba lamarin da ya yi kamari sai da  aka zauna a fadar Okimama na Ikom aka tashi baram-baram zaman da na wannan Asabar din ma da ta gabata aka sake tashi dutse hannun riga har ma daya daga cikin wanda ake zargi da kulla munafuncin Yahaya mai zaman sakatare ya zazzagi wakilin gwamnan Kuros Riba mataimaki na musamman kan harkokin baki Barista Musa Abdullahi Maigoro, ya yi barazanar tura masa tsageru da kuma rayuwarshi sai da wani basarake a fadar ya shiga tsakani.

Zargi na biyu da kitsa yadda za a takura masu saye da sayar da kayan gwari da suke zuwa daga jihohin Kaduna Kano da kuma Abuja kowace shekara suna biyan kudaden ka,idan ga masu gari da kuma gwamnati wannan shekarar kuma kamar yadda suka koka wa  wakilinmu cewa “su wadancan da suke son tilasta mana shiga kungiyar su sun hada baki ne da sarakunan gargajiiyar su 11 da kuma manyan ‘yan siyasar  garin da ma shugaban karamar hukumar Ikom cewa kowane sati za su rika ba su kudi Naira Milyan daya su raba idan kasuwar ta fara,mu kuma kuka ki yarda domin mun san zalunci ne saboda daga cikin su duka babu wani wanda yake wannan sana’ar tamu, sannan  kuma sun ce dole ba mu da ‘yancin shiga Kamaru mu sayo kaya sai dai mu ba su kudi su saya mana su rika yi mana fito kana kuma kowane Kwando za su karbi Naira 500 . Mu kuma muka duba muka ga zalunci ne tsagwaro shi ya sa muka ki yarda”.

Wata majiya da ke kusa da masu son yin zaluncin da ta bukaci sakaya sunanta ta shaida wa wannan jarida cewa “sun bi sarakuna da kuma shugaban matasa sun ba su kudi Naira dubu 20.kowannne su domin a matsa mana mu shiga kungiyar zalunci da za a rika ba su Milyan daya kowane sati”inji majiyar.

Zaman na ranar Asabar din an tashi baram-baram shi ne daya daga cikin sarakunan ya shaida wa Sarkin Hausawan Ikom Alhaji Tanimu Adamu Boyi cewa suke su sasanta da mutanensa a dawo a sake zama tun kafin a waste daga dakin taron da ke fadar basaraken sai da sarakunan da shugaban matasa suka rika cika baki duk wanda ba zai shiga kungiya ba ya  fita ya bar masu garin su Alhaji Sani Mika’ilu Sarina da aka fi sani da suna Alhaji Sani Bilanda shi ake harara ake zargi ake kuma ganin da laifi domin yaki ya amince da kungiyar zalunci.

Gaskiya Ta Fi Kwabo  wadda ta halarci zaman na tattaunawa a fadar basarake Okimama bangarorin biyu masu matsa lamba a kafa kungiya da kuma masu kinta kowa ya je ya zauna da bangarensa,  bangaren Alhaji Bilanda da ba su son shiga kungiyar sun fito karara sun nuna ta hanayar Sarkin Hausawan Ikom Alhaji Adamu Boyi maimakon bisa zalunci idan sun shiga kungiya su rika biyan Naira dubu 50 kowace mota suka ce su Naira dubu 10 kacal za su iya biya kamar da kana kuma sun amince za su ci gaba da biyan kudin kungiya amma sauran wahalhalun boda wato kan iyaka a kyale su za su yi sannan kuma a kyale su su rika shiga Kamaru suna sayo kayan su da kansu matukar mutum yana da fasfo da takardar iznin shiga kasar.”Za mu ci gaba da biyan kudin haulage da na karamar hukuma da kuma na tsaftace gari, sauran su ne kudin matasa,da na saukale,har ma da kukin hanya abin da muka sani kenan “inji su.

Wani abu da su ‘yan kasuwar suka ki amincewa da shi sh ine bijirewa dama da kundin tsarin mulki na kasa ya bayar kowane dan Nijeriya na da ikon zuwa ya yi kasuwanci ko ina a Nijeriya da su ‘yan Ikom suke son korar Hausawa a garin.Kafin wannan rana labarin da ya riski wannan jarida shi ne su ‘yan kungiyar dillalan tumatiri da kayan gwari wata mota da ta kawo tumatiri daga Kamaru sun kama kayan Alhaji Haladu ne suka ce sai an biya su Naira dubu 250 haka aka yi ta tirka-tirka sai dubu 150 aka ba su mai kaya kuma ya yi kara wajen ofishin kwamandan shiyya na ‘yan  sandan  Ikom  wajen ,yan sanda aka kama su.

Ya zuwa rubuta wannan labari har yanzu a iya cewa ba a kai ga cimma matsaya ba domin wakilinmu ya  samu labarin kwamandan shiyyar Ikom na rundunar ‘yan sandan Nijeriya  ya kirawo bangarorin biyu, sun zauna  bayan sakon jan kunne  da ya  aike masu a kyale kowa ya shiga Kamaru ya  sayo kayansa kamar yadda aka saba bayanin zaman ne dai bai kai ga kunnen wannan jarida ba.

Wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ta shaida wa wakilinmu a Ikom cewa “su dama ‘yan asalin garin kaska suke zame wa baki idan bako ya ki su zalunce shi korarsa suke yi kana kuma idan ma mutum bai yi hattara ba kudin hayar gida ko shago ma mutum sai ya yi biya biyu, ko ma fiye da shekara saboda kowace kungiya za ta zo da sunan ta kungiyar karbar haraji “.inji majiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here