Muhammad Saleh, Daga Yola
A karo na tara jami’ar Amurka da ke Najeriya (AUN) ta yaye dalibai kimanin 150, inda aka shawarci daliban da su yi aiki da kwarewar da suka samu wajen zama mutanen da duniya za ta yi alfahari da su.
Da take yi wa daliban jawabi shugabar jami’ar Farfesa Legene Quesenberry, ta ce duk ilimin da ba a yi amfani da shi ba tamkar babu ne, ta kuma yaba wa malaman jami’ar bisa kokarin da ta ce suke yi wajen bai wa daliban ilimi mai inganci.
Haka shi ma babban bako mai jawabi a bukin yaye daliban Ike Chioke, ya hori daliban da su yi amfani da kwarewarsu wajen shawo kan matsalolin tattalin arzikin da kasashen Afrika suke ciki.
Ya ci gaba da cewa kasashen duniya musamman kasashen yankin Afrika sun fada cikin matsin tattali arziki, sai ya jaddada bukatar cewa ilimin da daliban suka samu dama ce ta aiki tukuru domin ceto kasashen daga yanayin matsin da suke ciki.
Ya ce “tarihin shugabannin da suka gabata ya tabbatar cewa ba su dogara gaba daya bisa man fetur ba ne”.
Daliba mafi shahara a bukin Immaculate Onyinye, ta yaba wa hukumar gudanarwar jami’ar bisa damar da ta ce ta ba su na ganin sun zama wani, ta ce za su yi amfani da damar da suka samu yadda ya dace.
Ta kuma yaba wa kokarin jami’ar na ganin ta samar da musamman wajen bai wa daliban horo a bangarori daban-daban na ci gaban al\’umma.
Jami’ar AUN dai jami’ace da dalibai daga kasashen duniya daban-daban har kimanin 36, wacce aka kafa a shekarar 2003, ita ce dai jami’a mafi ci gaba a yankin da ake sa ran za ta taimaka wajen samar da shugabanni a kasashen yankin na Afrika.