Gina Otal A Legas: Yarfe Ne Aka Yi Wa Gwamna Yari

0
854
Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna
BIYO bayan irin yadda kafafen yada labarai suka rika wallafa labarin cewa shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya Alhaji Abdul\’aziz Yari Abubakar ya gina wani katafaren otal a unguwar Lekki da ke birnin Legas, mai magana da yawun Gwamnan Ibrahim Dosara ya bayyana a wani rubutun da ya saka a shafinsa na Facebook cewa Gwamnan bai gina otal din ba.
Ibrahim Dosara ya saka bayanin nan a shafinsa na facebook bayanin da shi ma ya samu daga ofishin kungiyar Gwamnonin Nijeriya cewa hakika labarin ya zama abin damuwa kwarai.
Ta yaya za a ce Gwamna ya gina otal na Dala Miliyan uku a Legas?
Duk da yake kamar yadda aka rubuta wai lamarin ya bulla ne daga hukumar EFCC a Legas, Gwamna Yari ya bayyana cewa shi ba shi da ko da fili ne a Legas ba wai otal ba.
Amma EFCC ta ce kamar haka\” sun samu otal da aka gina kan kudi Dala Miliyan uku da aka dauki kudin daga kudin bashin kulab din Faris wanda aka dawo da su Nijeriya kuma gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi.
Kuma an ji  Ibrahim Dosara a kafar Talbijin ta TVC mai mazauni a Legas yana bayanin musanta ginin otal din na makudan kudi.
Ya zuwa yanzu dai jama\’a suna ta bayyana albarkacin bakinsu game da wannan lamari musamman ganin cewa Dosara ya saka rubutun da ya samu daga ofishin kungiyar Gwamnoni ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here