Rabo Haladu Daga Kaduna
\’YAN matan Chibok 82 aka ceto ranar 6 ga watan Mayu gwamnatin Najeriya ta ce wata yarinya daga cikin \’yan matan Chibok da suka rage a hannun kungiyar Boko Haram ta tsere daga hannun kungiyar.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan, inda mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a wajen taron majalisar minsitoci a jiya Laraba.
An yi amannar cewa wasu sojoji ne suka tsince ta a lokacin da ta tsere tana hanyar guduwa
Mista Adesina ya kara da cewa sai dai kuma ba a yi wani karin bayani kan ko wace ce ita ba, ba kuma a fadi a halin da aka tsince ta ba.
Kun san \’yan Chibok ɗin da suka ƙi yarda su koma gida?
Na fi son zama a hannun Boko Haram— \’Yar Chibok
Kun san \’yan matan Chibok din da aka ceto?
A ranar 6 ga watan Mayu ne kungiyar Boko Haram ta sako \’yan mata 82 na makarantar sakandaren Chibok din, bayan sasantawar shiga tsakanin gwamnati da kungiyar Boko Haram din da wasu kungiyoyi da kasashe suka yi