ABIN TAUSAYI: \’YAN BINDIGA SUN KASHE WANI MAGIDANCI DA IYALANSA A JIHAR OGUN

0
850
Daga Usman Nasidi
WASU ‘yan bindiga da ake zato masu kisan gilla sun kashe wani iyali su 6, mai gidan da matarsa da kuma yara hudu a gidansu da ke Atiba yankin karamar hukumar Odogbolu a Jihar Ogun.
Akwai rashin tabbas kan dalilin kisan mutumin wanda aka gano a matsayin Sheikh Yusuf Abdulsalam Tanimola, wanda yake da kimanin shekaru 30, matarsa da \’ya\’yansa.
Rahotanni sun bayyana cewa biyu daga cikin yaran suna da shekaru biyu da haihuwa kuma tagwaye.
Jami\’in hulda da jama\’a na \’yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu bai samu cikakken bayani game da sunayen mutanen ba, amma ya tabbatar da al’amarin da ya faru a cikin dare.
Ya bayyana amincewa da cewa \’yan sanda za su yi iya kokari don kama wadanda suka aikata kisan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here