MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
KUNGIYAR Katsinawa mazauna Jihar Ribas ta shirya wa ‘ya’yan kungiyar da suka zo Fatakwal taron kara wa juna sani na kungiyar shugabannin makarantun sakandare ta kasa wato Ancopass liyafar ban-girma a garin Fatakwal .Shugaban kungiyar Alhaji Lawal Abdullahi Funtuwa ne ya sanar da haka a hira dawakilinmu na kudanci .
Ya ce mun shirya wa malaman namu liyafar ban-girma ne domin “mun karbi bakuncin malaman namu wadanda suka zo daga Jihar Katsina taron kara wa juna sani da aka yi na shugabannin makarantun sakandare a Fatakwal hedkwatar Jihar Ribas musamman ganin cewa su ne wadanda suka ilmantar da mu lokacin muna makaranta”.inji shi.
Alhaji Abdullahi Funtuwa ya ci gaba da cewa “wannan ba sabon abu ba ne ga kungiyar Katsinawa mazauna Jihar Ribas na karrama duk wani Bakatsine da ya zo Kurmi ziyara ta aiki kuma ya kawo ziyarar sada zumunci don haka ne ba su kasa a gwiwa ba karkashin jagorancinsa suka karrama bakin nasu.Ban da wannan ma ya ce hatta sauran kungiyoyin ‘yan asalin arewacin Nijeriya mazauna Ribas suna zaune lafiya da su ana mutunta juna .
Kungiyar Katsinawa mazauna Jihar Riba wadda ta shafe shekara sama da 25. Inji shugabanta suna taimaka wa duk wani dan dungiyar da kuma dan asalin Jihar Katsina mazaunin Jihar Ribas da sana’a da kuma duk wani taimako da ya kamata a yi masa ko ya bukata matuka bai saba kundin tsarin mulkin kasa ba da kuma na kungiyar su.
A cewar shugaban Katsinawan Ribas “ko lokacin da aka rika kai hare hare na ta,addanci fadan boko haram da aka yi a wasu sassana arewa maso gabas kungiyar su ta yi namijin kokari wajen yin rajista duk wani bako da ya zo dan Jihar Katsina fatakwal kana kuma sun bai wa hukuma hadin kai wajen tabbatar da cewa cikin su ba a samu bata gari ba.”
Kungiyar katsinawa mai dimbin tarihi da aka kafa kungiyar ce mai dumbun tarihi wadda akalla an shekara 25 da kafata, shugabanta na farko shi ne Alhaji lro Dabai Sarkin Hanji. Manufar Kungiyar ita ce kare muradu na jama’armu da kuma kare hakkokin jama’armu da ma taimakon juna.
Shugaban ya bayyana matukar farin cikinsu game da kyautatawa malaman nasu da suka ziyarce su suka yi ya kara da cewa “duk wata hidima da dalibi ya yi wa malaminsa ai bai biya shi ba wanda Allah ne kadai ne zai iya biyansa.
Karshe ya yi kira ga matasan kasar nan da kuma na Jihar Katsina a duk inda suke “ ina kira ga matasanmu da su zama masu girmama malamai da kuma shugabanni kuma mu yi masu addu\’a.ta alheri”.Domin babu wani abu da muke da shi da za mu iya saka masu da shi kan ilmin da suka ba mu face yi masu addu’a ta gari.inji Abdullahi Funtuwa.
A nasa jawabin mar habun lale da bakin tsohon shugaban kungiyar wanda a yanzu shi ne uban kungiyar, Alhaji Iro Dabai sarkin hanji Fatakwal ,ya yi addu’a yadda Allah ya kawo bakin Kurmi lafiya ya mayar da su gida lafiya, kana kuma ya jaddada muhimmancin sada zumunci tsakanin al’umma wanda a cewarsa dama dabi’a ce ta mutanen arewa da kuma Katsinawa “shi ya sa ma ake mana kirari da Katsina dakin kara”inji Iro Dabai.
Da take jawabin godiya a madadin Katsinawan da suka zo ziyarar aiki suka kuma sada zumunci shugabar kungiyar taron shugabannin makarantun sakandare ta Nijeriya Ancopass Dokta Hajiya Rakiya M. Inuwa ta gode wa daukacin shugabannin kungiyar da kuma yan asalin Jihar Katsina mazauna Jihar Ribas bisa namijin kokarin da suka yi na shirya masu liyafa tare da karrama su wannna a cewarta ba karamin nuna halayen Katsinawa nagari suka yi nba gida da waje hakan kuma injita ya nuna su jakadun jihar Katsina ne nagari dama makarantun da suka yi a jihar Katsina kwata.Ta roki Allah ya saka masu da alheri.