Samun Dangote Na Yini Daya Zai Ciyar Da Talakan Nijeriya A Shekara

0
1018

Rabo Haladu Daga Kaduna
RAHOTON mai taken \’Rashin Daidaito a Najeriya\’ ya bayyana wagegen gibin da ke tsakanin mawadata da talakawa da yadda wasu attajirai kalilan suka kankane tattalin arzikin kasa su kadai.
A cewar rahoton, mutum biyar da suka fi kowa wadata a Najeriya sun mallaki dukiyar da za ta iya raba al\’ummar kasar gaba daya da talauci.
Rahoton ya gano cewa mutumin da ya fi kowa wadata a Najeriya yana samun kudin da ya ninka na talakan kasar sau 8,000 kuma kudin na iya biyan bukatun talakan na shekara guda.
Kididdigar da wasu cibiyoyi ciki har da mujallar Forbes suka yi a baya dai ta nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ne ya fi kowa wadata ba kawai a Najeriya ba, har ma a daukacin nahiyar Afirka.
Rahoton ya kuma ce fiye da mutane miliyan 112 na fama da talauci a Najeriya, amma attajiri mafi arziki a kasar zai dauki shekara 42 kafin ya kashe kudin sa, idan yana kashe dalar Amurka miliyan daya a kullum.
Akwai dumbin masu kudi a Najeriya amma duk da haka akwai wadanda ke fama da talauci
Haka kuma a cewar Oxfam Nigeria, duk da cewa tattalin arzikinta yana kara habaka, Najeriya tana cikin kasashen da suka fi yawan masu fama da talauci a duniya. Alkaluma sun nuna cewa talakawa sun karu daga miliyan 69 a shekarar 2004, zuwa miliyan 112 a shekarar 2010 – karin kashi 69 cikin 100. Yawan miloniyoyi kuwa ya karu da kashi 44 cikin dari a wannan lokacin da rahoton ya duba.
Za a rage wa \’yan Nigeria miliyan 8 raɗaɗin talauci
\”Yadda nake fama da talauci\”
Arewa maso yammacin Nigeria ya fi talauci — Rahoto
Celestine Okwudili Odo ne babban jami\’i mai kula da shirin tabbatar da adalci a kungiyar ta Oxfam Najeriya.
A cewarsa, \”Babu tsafta a ce mafi wadata a Najeriya ya tara kudin da ba zai iya kashe su ba, a kasar da mutane miliyan biyar za su fuskanci matsaloli wajen samun abin da za su ci a bana. Bambanci tsakanin masu shi da talakawa yana kara ta\’azzara talauci, ya janyo koma-baya ga tattalin arzikin kasar, kuma yana kawo tashe-tashen hankula. Dole shugabannin Najeriya su tashi tsaye don kawar da wannan mummunar matsalar.\”
Rahoton ya kuma ce kashi 69 cikin dari na jama\’a na rayuwa ne da kasa da abin da ya kamace su a yankin arewa maso gabas, yankin da yunwa tafi tasiri, idan aka kwatanta da yankin kudu maso yamma, yanki mai karfin fada-a-ji a siyasance, inda a nan kashi 49 cikin dari ne kawai na jama\’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here