Daga Usman Nasidi
WASU jami’an rundunar \’yan sandan Najeriya sun wuce gona da iri yayin da wani faifan bidiyo ya nuna yadda suke cin mutuncin wani mutum a ranar Lahadi 14 ga watan Mayu a Jihar Edo.
\’Yan sandan dai sun daure mutumin da ankwa ne a jikin kofar motarsu ta waje, sa’annan suka dinga jan shi a kasa yayin da motar ke tafiya.
A cewar Franklyn, \’yan sandan sun yi masa duka, shi da abokinsa yayin da suka yi kokarin ceton wani matashin daga hannunsu.
“Yan sandan Najeriya sun yi mana duka, sakamakon magiyar da muke yi musu a kan su sake wannan matashin da suka daure da ankwa suna jan shi a kasa,hakan kuwa ya faru ne a ranar Lahadi 14 ga watan Mayu a cikin kwaryar birnin Bini na Jihar Edo” inji Franklyn.