Guguwa Mai Karfi Ta Kashe Mutum Uku A Sakkwato

0
866

Rabo Haladu Daga Kaduna

WATA guguwa mai karfin gaske ta yi sanadin  mutuwar mutane uku a inda  Jami\’in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa, NEMA,Suleiman Muhammed mai kula da jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi ne ya bayyana haka.
Ya ce lamarin ya auku ne ranar hudu ga watan Mayu na bana, inda guguwar ta ruguza gidaje fiye da gida 1,000 a kananan hukumomin Shagari da Tambuwal.
Jimillar gidaje sama da 1,000 sun rushe a kananan hukumomin Anka da Maradun da Birnin Magaji. Daga watan karshen watan Afrilu na bana zuwa yanzu, guguwar ta shafi jihohin Kebbi, Sakkwato da Zamfara.
\”Idan annoba ta faru, da farko za mu je mu tabbatar da tsaro a gurin, kuma mu kididdige yawan barnar, sannan mu rubuta rahoton irin taimakon da suke bukata\”, in ji jami\’in.
Guguwar ta haifar da asarar dukiya mai yawa.
Suleiman Mohammed ya ce \”Idan aka kiyasta abin da ya shafi Sakkwato da Zamfara ya kai sama da Miliyan 100 na Naira.\’\’
Jami\’in ya bayar da shawarar hanyoyin magance aikuwar irin wannan lamarin nan gaba, inda ya ce \”Shuka itatuwa zai taimaka wajen rage asara irin wannan nan gaba\”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here