Tsananin Kishi Uwar Gida Ta Kusa Halaka Mijinta Da Amaryarsa A Kaduna

0
1091
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SAKAMAKON mugun bakin kishin da wasu mata marasa hankali da tunani suke yi, ya sa wata mata kona mijinta tare da amaryarsa baki daya kamar yadda za ku iya gani a wannan hoto na rahoton wakilinmu.
Lamarin dai ya faru ne a Unguwar Malalin Gabas da ke cikin garin Kaduna, inda wata mata saboda bakin kishi a tsakar dare wannan amarya tana kwance ita da mijinta a daki sai uwar gidan ta bude kofa ta same su a kwance nan take ta watsa masu kananzir ta kuma kyasta ashana ta jawo dakin ta saka kwado, inda wuta ta kama dakin gadan-gadan. Sakamakon ganin hakan ne jama\’a suka kawo gudunmawa kuma da kyar aka balle dakin.
Nan take aka ruga da su babbar asibitin cikin birnin Kaduna inda ake kokarin ceton ransu.
Saboda faruwar wannan lamarin ne ya sa wadansu mutane yin kiraye-kirayen su san irin matar da za su aura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here