\’Yan Wasan Taraba FC Sun Yi Zanga-zangar Lumana Kan Hakkokisu

    0
    787
    Daga Usman Nasidi
    AN share sama da sa’o’i uku ana garkuwa da masu asubanci don motsa jiki da kuma jami’an ma’aikatu da ke cikin harabar filin wasannin zamani na Jolly Nyame a Jalingo fadar Jihar Taraba.
    An yi hakan ne sakamakon zanga-zangar da kungiyar kwallon kafa ta Taraba FC na neman a biya su hakkokinsu.
    Kungiyar ta shiga zanga-zangar neman biyan ta kudaden alawus na wata takwas da ‘ya’yan ta suka ce suna bin gwamnatin jiha wadda ta jefa su cikin matsanacin halin rayuwa da ba su iya biyan muhimman bukatunsu ba tare da kira ga gwamnati ta biya su hakkokinsu in ya so bayan haka ta rufe kulob na kwallon kafar idan ba za ta iya gudanar da ita ba kamar yadda wasu da suka nema a sakaya sunansu suka bayyana.
    Rahotanni sun bayyana cewa wannan zanga-zanga na baya-bayan nan shi ne na uku a kasa da shekara daya, wanda sai kungiyar ta tada jijiyar wuya ake biyansu wani kaso daga cikin alawus din da suke bin gwamnati, dalili da ya sa Muryar Amurka ta tambayi kwamishinan wasanni na jihar Taraba Rabaran Gambo Nbafor matakan da suke dauka na magance matsalar wanda ya danganta da matsin tattalin arziki amma ya ce suna yin duk kokarin da ya wajaba.
    Daga cikin masu asubanci don motsa jiki a filin wasannin zamani na Jolly Nyame da kungiyar kwallon kafar ta yi garkuwa da su na tsawon sa’o’i uku, akwai mai bai wa Gwamnan Jihar Taraba shawara kan harkokin labarai Silvanus Giwa da ya sha da kyar. Ya shawarci ‘ya’yan kungiyar su bi hanyoyin da tsari ya tanada wajen neman hakkokinsu.
    Kungiyar kwallon kafa ta Taraba FC ta yi barazanar kaurace wa wasanni na gaba idan gwamnati ta ci gaba da rike hakkokinsu a gasar rukunin kwararru na kwallon kafa ta kasa da yanzu ke zagaye na farko.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here