AN CAFKE WANI FASTO DA KWANYAR MUTANE A GARIN IBADAN

0
795
Daga Usman Nasidi
AN gurfanar da wani mutum mai shekaru 55 wanda aka sani da Fasto Ishaya a kotun majistare da ke Iyaganku a garin Ibadan da kwanyar mutane da wasu bokanci abubuwa.
Wanda ya gabatar da kararraki, Mista Lahadi Ogunremi yana tuhumar Faston ne a kan mallaki kwanyar mutane a ranar 5 ga watan Mayu daidai da karfe 9:10 na dare a hanyar titin Sango da ke Ibadan,
Ya bayyana cewa, laifukan sun saba wa sashe na 329 (A) Criminal Code Cap 38, Vol. II, a dokar Jihar Oyo na Najeriya, 2000.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin a cikin jawabinsa ga ‘yan sanda ya bayyana cewa shi Fasto ne daga wani cocin na ‘yan farin tufa a Legas. Faston ya kara da cewa bai kammala karatunsa ba kafin abokinsa ya jawo shi shiga yin aikin fastoci.
A cikin kalmomi Ishaya, ya ce: \”Ina amfani da Kakakin (wanda aka samu a mahallinsa) ne domin na iya juye mutanen da suka zo yin addu’a a wajena don iya samu zuzuruntun kudi daga gare su.”
Ya ce: \”Na samu kwanyar ne daga wani fanni a Legas, a lokacin da aka kawo wani injin buldoza da ke aiki a wani titi, sai na dauki kwanyar don na san zai yi min amfani.”
Jami’an ‘yan sanda suka cafke faston a hanyarsa daga Legas zuwa Ibadan a lokacin da ‘yan sandan ke bincikan jakunkunan mutanen da ke cikin motar.
Baban mai shari’a a kotun, Cif Majistare Abiola Richard dai ya bada belin Faston a kan kudi 75,000 da kuma mutane biyu a matsayin shaidu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here