Isah Ahmed, Jos
DAN majalisar dokoki ta Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Lere ta yamma Alhaji Bashir Gatari Idris ya tallafawa al\’ummar mazabarsa da takin zamani da irin shuka da maganin feshi don karfafa masu gwiwa kan shirin a koma gona. Dan majalisar ya tallafa wa al\’ummar mazabar tasa ne a wajen wani gagarumin taro da aka gudanar, a garin Ramin Kura a ranar Lahadin da ta gabata.
Da yake jawabi a wajen shugaban majalisar dokoki ta Jihar Kaduna Alhaji Aminu Abdullahi Shagali ya bayyana cewa a gaskiya wannan abu da wannan dan majalisa ya yi, na tallafa wa al\’ummar mazabarsa kan komawa gona ya yi daidai, domin a duk Jihar Kaduna babu yankin da ake yin noma kamar wannan yanki na Lere.
Ya yi kira ga \’yan majalisar dokoki ta Jihar Kaduna su yi kokari su rika tallafa wa al\’ummominsu domin basu kai matsayin da suke ba kai yanzu ba, sai da al\’ummominsu suka zabe su. Don haka ya kamata mu \’yan majalisa, mu riqa kyautatawa mutanen da suka zabe mu.
Shi ma a nasa jawabin tsohon shugaban karamar hukumar Lere kuma tsohon sakataren hukumar agajin gaggawa ta Jihar Kaduna Alhaji Aliyu Sale Ramin Kura ya yi bayanin cewa babu shakka wannan gwamnati ta yi kokari a matakin kasa da matakin jihohi musamman kan zaman lafiya.
Har\’ila yau ya ce gwamnatin nan ta sami gagarumar nasara kan mayar da kasar nan kan harkokin noma. Ya ce babu shakka kasar nan ta sami alheri mai tarin yawa sakamakon wannan kokari da wannan gwamnati ta yi.
\’\’A yau manomi yafi karfin ma\’aikaci a kasar nan. kuma yanzu mutane suna zaune lafiya don haka mun godewa wannan gwamnati. Kuma ina yaba wa abin da wannan dan majalisa ya yi na wannan tallafi da ya bayar. Wannan tallafi ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa. Don haka muna kira ga duk wadanda suka sami dama suyi kokari su yi wa jama\’a irin
wannan abu\’\’.
Tun da farko a nasa jawabin dan majalisar dokokin ta Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Lere ta yamma Alhaji Bashir Gatari Idris ya bayyana cewa an shirya wannan taro ne don a tallafa wa al\’ummar wannan mazaba da takin zamani da irin shuka da maganin feshi da injinan feshi don karfafa masu gwiwar komawa gona musamman ganin wannan lokaci ne na
faduwar damina.
Ya ce kowa ya san al\’ummar wannan yanki sune kan gaba a aikin gona a Jihar Kaduna musamman noman masara. Don haka ne aka tallafawa masu don kara karfafa masu gwiwa su ci gaba da dogara da kansu.
Ya ce wannan takin zamani tan 90 kyauta ya tallafa wa al\’ummar wannan mazaba. Ya ce wadanda suka amfana da wannan taki sun hada da shugabannin jam\’iyya da hakimai da malamai da fastoci da kuma matasa.
Alhaji Bashir Gatari ya yi bayanin cewa baya ga wannan tallafi ya tallafa wa matasa da dama kan harkokin ilmi da koyon sana\’a da gyara rijiyoyin burtsatse da sayen tarakunan wutar lantarki da dama a wannan mazaba. Ya ce babban burinsa shi ne ya ga cewa wannan mazaba ta sami ci gaba.