GWAMNATIN FILATO ZA TA KASHE NAIRA BILIYAN 18 WAJEN GINA HANYOYI A JIHAR

0
700
Isah Ahmed, Jos
GWAMNATIN Jihar Filato za ta kashe kudi sama da Naira Biliyan 18 wajen gina hanyoyin mota a sassa daban daban na jihar a kasafin kudinta na wannan shekara ta 2017. Kwamishiniyar kudi ta jihar Misis Tamwakat G. Well ce ta bayyana haka a lokacin da take yi wa \’yan jarida karin bayani kan kasafin kudin jihar, bayan da majalisar dokokin jihar ta
amince da kasafin kudin.
Har ila ta ce a wannan kasafin kudi an ware Naira Biliyan 11 don bunkasa harkokin ilmi a jihar. A inda aka warewa jami\’ar  jihar Naira Biliyan 5 don gudanar da ayyuka a jami\’ar jihar. Haka kuma aka ware wa hukumar kula da ilmin makarantur fimare ta jihar Naira Biliyan 1 da Naira Miliyan 800 don gina azuzuwa da samar da kayayyakin aiki a
makarantun firamare na jihar.
Hakazalika ta ce an ware wa ma\’aikatar gona kudi sama da Naira Biliyan 6 don bunkasa harkokin noma a jihar. Ta hanyar sanya tallafi  kan takin zamani da taraktocin noma da sanya a hannu a shirye-shiryen da suka shafi aikin noma don tallafa wa manoman jihar.
Ta ce an ware wa harkokin kiwon lafiya kudi Naira Biliyan 4 da sama da
Naira Miliyan 400 don gyara asibitoci da sayo kayayyakin aiki a asibitoci daban-daban na jihar.
 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here