AN SAKE KAMA WATA KWANTENA MAKARE DA MUGGAN MAKAMAI A IKKO

0
806
Daga Usman Nasidi Da Imrana Abdullahi
A mashigar ruwa ta kayayyaki da ke Tin-Can Island a jihar Legas, a yau da safen nan an kama kwantena ta kaya makare da muggan makamai domin shigo da su kasar nan, an dai waje kayan yakin da ya hada da bindigogi da albarusai a filin tashar, an kuma umarci kowanne ma\’aikaci da ya bar wurin cikin azama.
An dai sami tabbacin wawan kamun ta bakin kakakin hukumar kwastan reshen tashar, Mista Uche Ejesieme wanda ya ce jama\’a su kwantar da hankullansu, bayanai za su zo in sun gama bincike.
A kwanakin nan dai ana ta yamadidin zancen gwada hambaras da gwamnatin Buhari, ana kuma samun masu kokarin tada kayar baya a Neja-Delta da ma \’yan kabilar Ibo masu son kafa kasarsu. A hannu daya kuma masu yaki da sunan addini, Boko-Haram suka kara dagewa kan kokarinsu na kashe jama\’a.
A shekarar 2010 ma dai an kama irin wadannan makamai da aka tabbabar za su iya tada Jihar Legas gaba daya da an yi amfani da su, inda bincike ya nuna daga kasar Iran aka shigo da su don wata manakisa, amma daga baya Iran din ta ce kayan yaki ne take so ta tura kasar Gabon ba Najeriya ba. An kama wani Bafarishe da wani Basakkwace bisa lamarin, an kuma kaisu kotu a wancan lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here