AN TARWATSA GANGAMIN \’YAN SHI\’A DA BARKONON TSOWA DA RUWAN ZAFI A ABUJA

0
872
Daga Usman Nasidi
JAMI\’AN ‘yan sanda babban birnin tarayya Abuja, sun tarwatsa wani gangamin taron magoya bayan harkar musulunci ta kungiyar Shi\’a (IMN) domin yin kira kan a saki Zakzaky.
‘Yan sandan sun fesa wa masu taron gangamin ne ruwan zafi da barkonon tsohuwa domin tarwatsa su yayin da suke yin zanga-zangar a garin Abuja.
‘Yan kungiyar Shi\’ar  wato (IMN), sun taru a gaban ofishin hukumar kare hakkin bil adama domin nuna rashin jin dadin su yadda har yanzu ba a saki Zakzaky ba.
Wata majiya daga jami\’an \’yan sanda shiyar Abuja da ke birnin tarayyar a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu ta bayyana cewa sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da kuma ruwan zafi, domin hana magoya bayan kungiyar Shi\’ar gudanar da wani gangami a gaban ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da ke Abuja, wanda suka shirya domin yin kira kan a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Idan ba a manta ba, za a iya tunawa a baya sojoji sun yi wa gidan shugaban mabiya kungiyar \’yan uwa musulmi ta shia\’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kuma wasu mabiyansa da ke Husainiyya kawanya sanadiyyar wata rikici da ta barke a lokacin da Babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai yake wucewa ta kusa da inda mabiya Shi\’ar ke taro a cibiyar Husainiyya, inda aka tsare masa hanya, tare da kai masa hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here