Majalisa Ta Ba Da Umurnin A Cafko Tsohon Gwamnan Kebbi

0
919

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

MAJALISAR dokokin jihar Kebbi ta bayar da umarni ga rundunar \’yan sanda ta kasa da ta kamo tsohon Gwamnan jihar Alhaji Sa\’idu Nasamu Dakin Gari, a duk inda yake
Shi dai wannan umarni ya biyo bayan irin yadda tsohon Gwamnan ya yi mirsisi ya ki halartar majalisar duk da zargin aringizon kudin da suke yi masa kan wata kwangilar filin jirgin sama a jihar, kudin da suka kai Naira Biliyan 6.4 amma Dakin Gari ya kasa halartar majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here