AN BUKACI MUSULMAI DA SU FARA DUBAN WATAN RAMADAN DAGA YAU JUMA\’A

0
862
Daga Usman Nasidi
MAI alfarma Sarkin Musulmai, kuma shugaban majalisar koli ta malamai, NSCIA Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bukaci musulman kasar nan da su fara neman jinjirin watan Ramadan a ranar Jama’a, wato yau kenan.
Daraktan sha’anin mulki na NSCIA, Ustaz Isa Christian Okonkwo ne ya bayyana haka a jiya Alhamis 24 ga watan Mayu, inda ya taya al’ummar musulmai murnar karasowar watan Ramadan.
“Tun bayan azumin shekarar da ta gabata, kwamitin neman watan ya shawarci mai alfarma Sarkin Musulmai dangane da ganin wata da a dinga fitar da sanarwar ganin wata a kowanne wata. Don haka ne Sultan ya shawarci musulmai da su fita neman ganin wata a ranar 26 ga watan Mayu, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban.” Inji Ustaz Okonkwo
Sultan ya ce muddin an ga watan a daren Juma’a, jama’a su taimaka su sanar da sarakunan al’umma, don a sanar da ranar Asabar a matsayin daya ga watan Ramadan, idan kuma ba a gani ba, Lahadi 28 ga watan Mayu ya zama daya ga watan Ramadan 1438 bayan hijra.
Daga karshe sanarwar ta kara da shawartar musulmai da su jajirce wajen ribatan watan Azumin Ramadan.
Hakazalika, majiyarmu ta bayyana cewa an bada lambobin wayar wasu malamai da ya kamata a tuntuba kamar haka, Mallam Hafiz Wali 08036009090, Sheikh Tahir Bauchi 08032103733, 08033058201, Sheikh Kariballah Kabara 08035537382, Muhammad Nasir AbdulMuhyi 08065687545, 08024333381,
Sheikh Habeebullahi Adam Abdullahi Al-Ilory 08023126335 domin sanar da ganin jinjirin watan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here