ALLAH YA YI WA TSOHON GWAMNAN JIHAR GOMBE KANAR INUWA RASUWA

0
802
Daga Usman Nasidi
ALLAH ya yi wa Kanar Muhammad Inuwa Bawa mai ritaya tsohon Gwamnan Jihar Gombe na zamanin mulkin soja rasuwa .
Marigayin Inuwa Bawa dai shi ne Gwamnan Jihar Ekiti na farko daga watan Oktoba 1996 zuwa Agusta 1998, kuma ya kasance Gwamnan Jihar Gombe na biyu bayan samun jihar duk a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha daga watan Agusta 1998 zuwa Mayu 1999.
Marigayi tsohon Gwamnan Jihar Gombe Kanar Muhammad Inuwa Bawa mai ritaya ya rasu yana da shekaru 63 da haihuwa, ya rasu ne a ranar Juma\’a, 26 ga watan Mayu a wani asibiti a garin Jos babban birnin Jihar Filato, bayan yi masa tiyata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here