Muhammad Saleh, Daga Yola
WATA kungiyar magoya bayan tsayawa takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo a karo na biyu ta gudanar da taron ranar dimokuradiyya a Yola, inda ta jaddada goyon baya ga shugaban kasar.
Kungiyar ta kuma jagoranci gudanar da addu’o’in neman lafiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda kuma suka yi wa mukaddashin shugaban kasar addu’ar Allah ya ba shi ikon tafi da kasar yadda ya dace, da kawo sauki ga rayuwar jama’a.
Da suke gabatar da addu’o’in Malam Sani Jada da Rabaran Musa Kallamu, sun yi addu’ar Allah ya samar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al\’ummar kasar, game da halin matsin da ake ciki.
Da yake magana a taron shugaban kungiyar Buhari/Osinbajo 2019, Alhaji Yahya Hamman Julde, ya ce gwamnatin tarayya ta taka muhimmiyar rawar ganin da ya kamata a gudanar da buki.
\’Ya dace mu nuna farin ciki da godiyarmu ga Allah, bisa samun shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo wanda ya sa muke nan yanzu, muna neman Allah ya maimaita a kai ga gyara mana kasar baki daya”.
Shugaban ya kuma bayyana yaki da cin hanci da rashawa da samar da tsaro da kuma bunqasa harkokin noma da cewa suna daga cikin manya-manyan ci gaban da gwamnatin ta samu cikin shekaru biyu, don haka ya ce kamata ya’yi jama’a su goyawa gwamnatin baya.
Sauran da suka yi magana a taron sun hada da Alhaji Uba Dan arewa, Honarabul Rufa’i Gombi, Sanata Abdul’aziz Nyako da kuma Sanata Ahmad Mo-Allayidi, inda suka bayyana wasu nasarorin gwamnatin Buhari da nema mishi goyon bayan jama’ar kasar.
Comment:muna goyan baya