Mahauta Sun Tsira Da Kyar A Hannun Bata-gari Dalilin Bashin Da Ake Binsu

0
954

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

‘YAN kasuwa mahauta dake sayar da balangu da suya Acade da ke Layin Bagobiri Unguwar Hausawa  Kalaba Jihar Kuros Riba sun sha da  kyar yayin da wasu kuma suka jikkata a wani harbin kan mai uwa da wani da ake zargin wani mahauci jigo a kungiyar mahauta ta kasa reshen jihar  mai suna Raphael Edem Ukpong ya jagoranci yara eriya boyis suka yi ta harba-harbe a kasuwar tasu.

Shi Edem Ukpong dai yana bin mahautan abokan huldar su bashin kudi ne da harkar kasuwa ta hada su day an uwansa mahauta Magana har gaban ,yan sanda acan aka sulhunta tsakanin su har ma sunci gaba da rage bashi kudin da yake bin su kuma a cewar mahautan da suka zanta da wakilinmu na kudanci sun shafe wata 17.suna rage masa bashin wurin ‘yan sanda da ke hedkwatar  rundunar ‘yan sandan jihar ko wane wata kwatsam sai gashi ya jawo yara zauna gari banza sun zo sun hana su kasuwanci suka rika yin harbe harbe lamarin day a jawo masu asarar cikinin da suka yi da kuma kwashe masu na naman da suka gasa .

A wannan hali da wakilinmu ya ziyar ci layin suya acade ya iske mahautan sunyi jungun-jungun suna alhinin asarar da sukayi ta nama da suka gasa da kuma kudaden cinikin su da suka yi akalla rumfuna 50 a wannan kasuw akuma kowa ya gasa nama yana sayarwa jin wancan harbe harbe ne ya sanya masu dukiya da abokan ciniki da suka zo sayen nama kowa ya nemi hanyar da zai tsira da ransa samun waccan dam a ce bata-gari suka yi awon gaba da iya naman da suka diba wasu kuma suka zube a kasa.

Da yake yi wa wannan jarida karin bayani yadda lamarin ya faru jigo a  kasuwar  Alhaji Yusuf Ibrahim Chaba Rawaiya ya bayyana yadda aka tunzurasu “ Ranar Alhamis da yamma muna cikin kasuwancin mun kowa ya gasa namans ana sayarwa yana sayarwa kwatsam sai muji harbe-harbe yara yan eriya sun far mana mu da kayan su said a muka nemi dauki daga jami,an tsaro tukuna kura ta lafa”.Alhaji Ibrahim Chaba Rawaiyya ya ci gaba da cewa wanda ya yi jagoranci bata-gari suka yi mana wancan ta’adi ba wani ba ne face Raphael Edem Ukppong da yake bin mu bashi kuma yau tsawon wata 17 muna biyan kudin ko wane wata a ofishin ‘yan sanda da ke hedkwatar su tan an Kalaba”.

Daga bisani wakilinmu na kudanci yaji tabakin wasu da suka tafka asarar da kuma yadda ya mutsin ya shafe su farko Alhaji Sule Usman sokoto “ shi Edem ne ya jawo yara bata gari sukayi ta mana harbe-harbe kowa yab tsorata suka kwashe mana ciniki da kuma naman da muka gasa muke sayarwa”Shima Hashimu Rawaiyya da lamarin ta,addancin ya shafa ya ce “an kwashe mana kaya da kuma dukiya wadda sai an natsu ne za,a iya tantance asara da kuma kaddarar data bace mudai gashi muna cikin tsaka main yuw aamma muna rokon hukumar yan snada dasu shigo ciki tunda dama maganar na hannun su saboda kada wulakancin da aka mana ya sake faruwa.

Wata majiiya dake kusa da yan kasuwar wadda bata bukatar ko kadan a ambaci sunanta  ta shaidawa Gaskiya tafi kwabo cewa sunn aike da takardun koke zuwa ga Hafiz Mohammed Inuwa kwamishinan yan sandan jihar kuros riba da kuma jami,ain yan snadan dake rike da karar tasu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here