Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Da Gwamna Bindow Sun Nemi A Yi Wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Addu’a Ta Musamman

0
919

Muhammad Saleh, Daga Yola

KAMAR kowace jiha, jihar Adamawa ma ta gudanar da bukin ranar dimokuradiyya ta bana da jihohin kasar ke gudanarwa duk shekara, inda gwamnan jihar Bindow Jibrilla, ya bukaci  addu’a  ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, ya bayyana bukaci haka lokacin da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar, ya ce bisa la’akari da halin da shugaban yake ciki ya zama wajibi a ci gaba da gudanar mishi da addu’ar samun sauki.

“kamar yadda aka saba, a ci gaba da yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu’ar samun sauki, domin ya dawo ya ci gaba da ayyukan ci gaba da yake yi wa kasa, musamman mu a arewa maso gabas”.

Ya ce shugaban kasar ya taimaka wajan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin jihohin arewa maso gabas, ta yadda jama’ar yankin suna samun bacci yanzu ido rufe sakamakon samun zaman lafiya “ku rika yi mishi addu’a samun sauki”.

Shi kuwa da yake jawabi a taron tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, bukatar goyon baya da hadin kai jama’ar jihar, wanda ya bayyana da cewa zai taimaka wajan ci gaba da ayyukan ci gaban da gwamnan ke aiwatarwa.

Ya ce gwamnan jihar Bindow Jibrilla ya cancanci ya dawowa karo na biyu, domin ci gaba da gudanar da muhimman ayyukan ci gaban alumman da ya faro, ya ce  tun kafa jihar ba’a taba samun gwamnan da ya hade kan jama’ar jihar haka ba.

Ya ci gaba da cewa “Adamawa muna buqatar samun haxinkan da fahimtar juna tsakanin jama’armu, shine kuma abun da Bindow ya yi, wannan taron abin misali ne, mu hada kai domin samun ci gaba”.

Da dama dai da suka yi jawabi a taron kama daga Farfesa Jibrin Aminu, tsohon hafsan hafsoshin sojan sama Air Michal Alex Badde da tsohon gwamna Welbeforce Juta, Sanata Binta Masi Garba, tsohon Sanata Silas Zwingina, duk sun yaba wa gwamnan bisa ci gabar da ya samar cikin shekaru biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here