WATA MATA TA SAYAR DA YARANTA 4 DAGA CIKIN 5 A JIHAR LEGAS

0
945
Daga Usman Nasidi
JAMI\’AN ‘yan sanda sun kama Misis Vicky, wata matar gida a Lagas kan zargin cewa ta sayar da hudu daga cikin ‘ya’yanta biyar ga mutane daban-daban ba tare da sanin mijinta ba.
Mijinta ya aika takarda ga shugaban ‘yan sandan yankin ACP Austines Akika sannan kuma y aba jami’an ‘yan sanda umurnin kama ta.
Wata majiya ta bayyana cewa, tana sayar da yaran ne daya bayan daya sannan kuma ta yi nasaran sayar da hudu daga cikin yaran.
Da farko, ta yi ma mijinta karyan cewa ta kai yaran gurin ‘yan’uwansu ne har sai lokacin da mijin ya gano daga baya cewa tana sayar da yaran ne.
Rahotanni sun bayyana cewa ta sayar da na karshen a kan N400,000 sannan makwabta suka sanar da mijin wanda ya kai kara gidan ‘yan sanda aka zo aka kamata sannan aka tsare ta a kurkuku.
An rahoto cewa ta rigada ta fada ma ‘yan sanda gaskiya yayinda ake kokarin ceto yaran sannan kuma a kama wadanda suka siya yaran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here